Rasha ta ce, an kashe mata sojoji 63


Rasha ta ce, an kashe mata sojoji 63 a wani kazamin hari da Ukraine ta kaddamar kan dakarunta a karshen makon da aka gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara.

A cikin wata sanarwa da ba a saba ganin irinta, Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce, an kashe sojojin kasar 63 sakamakon wani harin makami mai linzami da Ukraine ta kaddamar kan birnin Makiivka da ke gabashin Ukraine wanda Moscow ta mamaye.

Wannan ne asarar sojoji mafi girma da Rasha ta yi tun bayan barkewar yaki tsakaninta da Uktraine a ranar 24 ga watan Fabairun da ya gabata.

Rasha ta ce, an yi amfani da shu’umin na’urar cilla makaman roka da aka kera a Amurka wajen kaddamar mata da wannan farmakin, yayin da a Babban Hafsan sojin Ukraine ke cewa, dakarunsu ne suka kai harin a Makiivka.

Ya kara daa cewa, sun lalata wuraren ajiyar makaman Rasha har guda 10 a yayin harin.

Tun da fari, Sashen Yada Labarai na Rundunar Sojin Ukraine ya yi ikirarin cewa, kimanin sojojin Rasha 400 ne suka mutu a Makiivka sabanin 63 da aka ba da rahoto.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki