Posts

Showing posts with the label Rahoton aikin Hajin 2023

Gwamnan Kano ya bayar da kyautar Miliyan daya, kujerar Haji da kuma daukar aiki na dundundun ga ma'aikacin wucin gadin hukumar alhazai

Image
Dayyabu Bala Gezawa (Dan Gezawa) shi ne ma'aikacin wucin gadin hukumar alhazai ta Kano da ya tsinci dala dubu 16 kudin guzurin maniyyatan wata kararmar hukuma gaba daya kuma ya damkasu ga Darakta Janar na hukumar  Gwamnan Kano ya bayar da kyautar Miliyan daya, kujerar Hajj da kuma daukar aiki na dundundun ga ma'aikacin wucin gadin hukumar alhazai da ya mayar da naira miliyan 16 ya guzurin alhazai da ya tsinta Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayar da wannnan kyauta ne a ranar Litinin, yayin taron mika masa rahoton aikin Hajin 2023 daga hannun Hukumar kula da Jin dadin Alhazai ta Jahar Kano Gwamnan wanda ya bayyana farin cikinsa bisa tarin nasarorin da sabon shugabancin hukumar ya samar a yayin aikin hajin da ya gabata, duk Kuwa da cewar sun tarar da tarin matsaloli dangane da shirin aikin Hajin Yace gwamnatinsa na bayar da cikakkiyar kulawa ta dukkanin lamarin da ya shafi Harkokin addinin islama, musammam ma aikin haji da ya kasance daya daga Cikin shikashikan musulinci