Gwamnan Kano Ya Kaddamar Da Aikin Gadar Sama Mai Musayar Hannu Kan Naira Biliyan 15 A Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aza harsashin samar da gadar sama musayar hannu kan kudi Naira biliyan 15 a kofar Dan'agundi da ke cikin birnin Kano a wani bangare na hangen nesa na inganta zirga-zirgar ababen hawa a tsohon birnin. Gwamnan wanda ya ziyarci wurin da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata tare da wasu mambobin majalisar zartarwa, ya tabbatar da ganin gwamnatinsa na ganin an mayar da tsakiyar birnin zuwa matsayin babban birni. Za a iya tunawa cewa Gwamna Yusuf a watan Disamba, 2023, ya ba kamfanin CCG Nigeria Limited aikin na biliyoyin nairori tare da umarnin kammalawa watanni goma sha takwas. An bayar da wannan ayyuka da yawa tare da wata gadar musanyar hannu a shataletalen Tal'du kuma a cikin tsakiyar gari, don sauƙaƙa cunkoson ababen hawa. "Mun kirkiro hanyoyin da za a iya amfani da su kuma ana sa ran masu ababen hawa za su bi ka'idoji don kare lafiya tare da ba da damar gudanar da aikin yadda ya kamata." Gwamna Abba Kabir ya kuma aza h...