Posts

Showing posts with the label NNPCL

Najeriya Za Ta Fara Fitar Da Tataccen Mai Kasar Waje A 2024 —NNPCL

Image
Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) Mele Kyari ya ce Najeriya za ta zama kasa mai fitar da tataccen man fetur da dangoginsa zuwa kasashen waje a shekarar 2024 mai kamawa. Mele Kyari ya kuma ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa cikin watanni uku masu zuwa ba za a samu karancin man fetur ba, kamar yadda ake gani a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara. “Ina tabbatar wa shugabannin majalisa ba za a fuskanci karancin mai ba. “Za ku ji ana ta yada labarin layuka a gidajen mai, amma ba gaskiya ba ne,” in ji Mele Kyari. Hukuncin da muka zartar na korar Gwamnan Kano na nan daram – Kotu Magoya bayan NNPP sun yi zanga-zanga kan hukuncin kotu a Kano Ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci shugabannin majalisar dattawa. Ya kara da cewa NNPC zai gyara matatar mai ta garin Fatakwal a wata mai kamawa, sannnan matatar mai ta Warri ta biyo baya a farkon 2024. Haka zalika, ya yi hasashen NNPCL zai samu ribar da ta kai triliyan biyu a shekarar 2023 da ke dab da karewa. Kyari ya shai

Kwana 6 Kafin Saukar Buhari NNPC Ya Ci Gaba Da Hako Mai A Borno

Image
Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya ci gaba da aikin hako danyen mai a yankin Tafkin Chadi da ke Jihar Borno, bayan shekara shida da dakatar da aikin. An ci gaba da aikin ne washegarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da Matatar Mai ta Dangote, wadda ita ce mafi girma a Afirka, wadda ake sa ran za ta taimaka wajen rage wahalar mai a Najeriya. Kamfanin NNPP na da kaso 20 cikin 100 na hannun jarin sabuwar matatar mai karfin samar da tataccen mai ganga 650,000 a kullum, mallakin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote. Matata dai sa ran masana’antar da ta biya bukatun man Najeriya 100% har ta ba wa wasu kasashe 12 na Afirka, inda ake hasashen za ta rikar da kashi 36 na man da ake bukata a nahiyar. Ana sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai halarci taron kaddamar da dawowar aikin Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno, ta intanet a ranar Talata, kwana shida kafin saukarsa daga mulki. A shekarar 2017 ne aka dakatar da aikin neman danyen mai a rijiyoyin man masu suna Wadi