Posts

Showing posts with the label Yajejeniya

Najeriya da Saudi Arabiya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan aikin hajjin 2024

Image
A yau 7 ga watan Junairu 2024 ne Najeriya karkashin hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta amince da gudanar da aikin Hajjin bana ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna ta shekarar 2024 (1445AH) da ma'aikatar aikin hajji da umrah ta kasar Saudiyya. A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace bikin rattaba hannun da aka yi a Jeddah ya samu halartar manyan wakilai daga Najeriya karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da Malam Jalal Ahmad Arabi, mai rikon mukamin Shugabancin NAHCON.  Tawagar kasar Saudia ta samu jagorancin Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dr. Taufiq Al-Rabiah.     Kafin rattaba hannu kan yarjejeniyar, Ministocin biyu sun yi wata ‘yar gajeruwar tattaunawa inda Najeriya ta bukaci a kawo karshen matsalar karancin tantuna a Mina tare da neman karin wasu sharuddan da suka dace ga dilolin Najeriya a lokacin jigilar ka