Search This Blog

Showing posts with label Nijar. Show all posts
Showing posts with label Nijar. Show all posts

Tuesday, 28 November 2023

Abin Da Ya Kawo Cikas A Sulhun ECOWAS Da Sojin Nijar — Yusuf Tuggar

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce sun yi tayin tattaunawa domin kawo ƙarshen tankiyar da ke tsakanin Ƙungiyar Raya Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da sojojin da suka kifar da Shugaban Nijar Mohammed Bazoum, amma hakan bai yiwu ba, don kuwa shugabannin sojojin sun ƙi amincewa da yunƙurin.

Ambasada Tuggar ya faɗi hakan ne a wata hirarsa da BBC, yana mai cewa duk wata magana da ta shafi a saki Shugaba Bazoum, sojin ba su amince da ita ba.

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 2 a Imo
Abdul Amart ya siya wa iyalan Aminu S. Bono gida
“Sun ce kar ma a yi wannan maganar, kar ma a sa shi cikin sharuɗɗan yin sulhu,” in ji Yusuf Tuggar.

Ya bayyana cewa babu ta yadda za a iya samun sulhu a wannan yanayi.

“Za su ci gaba da rike shi kenan ya yi zaman dindindin a kulle?”


Ministan ya ce sojojin da suka yi juyin mulki ne suka janyo wa Nijar takunkumin da ECOWAS ta ƙaƙaba mata, da kuma shiga halin da take ciki.

Ya ce abin da suke buƙata shi ne a saki Shugaba Bazoum.

“Muna son sojojin su saki Bazoum ya fita, a kai shi wata ƙasa daban. Ba maganar dawo da shi kan mulki ake yi ba,” in ji ministan.


Ya ƙara da cewa, duk wani yunƙuri da suka yi, sojojin sun ƙi ba da haɗin-kai ta kowanne yanayi, inda suka ce ba sa son a yi maganar ma kwata-kwata.

“Ta yaya za a yi sulhu a haka, mene ne sojojin za su yi saboda in ana son yin sulhu tsakanin mutane, gefe ɗaya zai ce ya haƙura da abu kaza, ɗaya gefen ma ya ce haka.

“To su kwata-kwata cewa suka yi, sai dai a yi musu abin da suke so,” in ji Tuggar.

Ya ce ECOWAS ba ta da matsala da ƴan Nijar kuma ba ta jin daɗin halin da suke ciki.

Ya ƙara da cewa matsalarsu ita ce sojojin da suka kama Shugaba Bazoum suka riƙe, duk da yake suna ganin akwai hanya mai sauƙi ta warware rikicin.

Ministan harkokin wajen Najeriyar ya ce dole ne idan mutane suka yi ba daidai ba a tsawatar musu.

A cewarsa, sojojin ma ba yadda suka iya da junansu don kuwa, kowa na ƙoƙarin samun ƙarfin iko a Nijar, inda a gefe guda suka bar ƴan ta’adda na can suna cin karensu babu babbaka.

Watanni huɗu bayan kakaba wa jamhuriyar Nijar takunkumi da ƙungiyar ECOWAS ta yi, sakamakon juyin mulkin sojoji, har yanzu ƴan ƙasar na ci gaba da ɗanɗana kuɗa da rayuwar ƙunci.

Farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi, saboda rufe iyakar ƙasar da Najeriya ta yi, da kuma yanke hulɗar kasuwanci da ƙasashen ECOWAS suka yi da Nijar.

(AMINIYA)

Friday, 20 October 2023

Mun Dakile Yunkurin Bazoum Na Tserewa Daga Nijar Zuwa Najeriya - Sojoji

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da daƙile wani yunƙurin hamɓararren Shugaban ƙasar Mohamed Bazoum na tserewa tare da iyalinsa.

Kakakin gwamnatin sojin Nijar, Kanar-Manjo Amadou Abdramane, wanda ya bayyana hakan cikin jawabin da ya yi wa jama’ar ƙasar ta Talabijin, ya ce Bazoum da iyalinsa sun tsara guduwa daga Fadar Shugaban ƙasar ne da misalin ƙarfe uku na dare.

Martanin tubabbun ’yan Boko Haram kan tuban muzuru
Kamfanin Nokia zai sallami ma’aikata 14,000 saboda rashin ciniki
Ya ce Mohamed Bazoum ya yi kokarin tserewa da karfe 3 na safiyar ranar Alhamis tare da iyalansa masu dafa masu abinci 2 da kuma jami’an tsaro guda biyu.

Sai dai a cewar sojojin, wannan yunƙurin da bai kai ga ci ba, na cikin wani tsari da aka shirya da kuma sojojin suka ce suke bi sau da kafa.


Kanar-Manjo Amadou Abdramane ya ce “matakin farko na wannan shiri shi ne na su fice daga cikin fadar zuwa kewayen wurin inda wata mota ke jiransu daga nan ne za a dauke su zuwa wani gida da ke cikin unguwar Tchangarey.

“Sannan daga nan kuma a nufi wani wuri inda wasu jirage biyu masu saukar ungulu na wata kasa da sanarwar ba ta bayyana ba za su kai su Birnin Kebbi da ke Najeriya.’’

Sanarwar sojojin ta kuma jinjina wa sojojin da hazakarsu da kuma himmar su ta ba da damar dakile wannan yunkurin tare da kare rayuka.

Ana tsare da Bazoum da matarsa da kuma ɗansa ne tun bayan da sojoji suka yi wa gwamnatinsa juyin mulki a cikin watan Yuli.


Tun bayan juyin mulkin ne aka raba gari tsakanin kasar ta Nijar da uwargijiyarta Faransa ta hanyar korar jakadanta da kuma sojojinta 1500 da ke yaki da kungiyoyin masu da’awar jihadi a yankin Sahel musaman a yankin iyakoki 3.

Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 24 ga watan Satumba Shugaba Emmanuel Macron ya ce Faransa za ta kwashe dukkan dakarunta da jakadanta da ke Nijar nan da karshen shekarar 2023.


Wannan na zuwa ne bayan Jakada Sylvain Itte ya fice daga kasar wata guda bayan sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum sun ba shi wa’adin awa 48 ya bar kasar bayan “ya ki amsa gayyatar ma’aikatar harkokin waje don halartar taron” da aka gayyace shi da kuma “wasu matakai da Faransa ta dauka da suka ci karo da muradan Nijar.”

Nijar dai na daya daga cikin kawayen kasashen yammacin duniya a yankin Sahel da suke yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai masu alaka da Al-Qaeda da IS.

A kan haka ne kungiyoyin yammacin Afrika irin su ECOWAS da UEMOA suka kakabawa kasar takunkumi domin tilastawa sojojin mayar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.



Sunday, 30 July 2023

Labari da dumiduminsa : Kungiyar ECOWAS ta yi la'akari da rikicin soji da 'yan juyin mulkin Nijar, ta bukaci a maido da shugaban kasa.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta ba da wa'adin kwanaki bakwai ga gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar da ta mayar da shugaban kasar...

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta ba da wa'adin kwanaki bakwai ga gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar da ta maido da shugaba Mohamed Bazoum a matsayin zababben shugaban kasa ta hanyar dimokuradiyya ko kuma ya fuskanci tsauraran takunkumi.

Kungiyar ta yankin ta kuma umurci dukkanin hafsan hafsoshin tsaro na kasashe mambobin kungiyar da su ci gaba da gudanar da wani taron gaggawa don tsara dabarun aiwatar da yuwuwar aikin soja na maido da tsarin mulki a ofis.


Kungiyar ECOWAS wacce ta amince da Bazoum a matsayin halastaccen shugaban kasar, ta yi barazanar sanya dokar rufe iyakokin kasa da hana zirga-zirgar jiragen sama a jamhuriyar Nijar matukar sojojin da suka kitsa juyin mulkin suka kasa kunnen uwar shegu.

Wannan shi ne kudurin babban taron hukumar shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS da aka gudanar a ranar Lahadi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.


A cewar shugaban hukumar ta ECOWAS, Omar Touray, wanda ya karanta sanarwar, kungiyar ta yi kira da a gaggauta sakin shugaban kasar Mohamed Bazoum a matsayin shugaban kasa kuma shugaban kasar Jamhuriyar Nijar tare da maido da tsarin mulkin kasar baki daya. a Jamhuriyar Nijar.

“Ku yi watsi da duk wani nau’i na murabus da ake zargin ya fito ne daga mai girma shugaban kasa Mohamed Bazoum; ya dauki matakin tsare shugaba Bazoum ba bisa ka'ida ba a matsayin garkuwa da mutane kuma yana rike da wadanda suka rubuta yunkurin juyin mulkin wadanda ke da alhakin kare lafiyar mai girma shugaban kasa Mohammed Bazoum, da kuma 'yan uwa da gwamnatinsa.

“Idan har ba a biya bukatun Hukumar cikin mako guda ba, a dauki dukkan matakan da suka dace don maido da tsarin mulki a Jamhuriyar Najeriya.

“Dakatar da duk wata huldar kasuwanci da hada-hadar kudi tsakanin kasashe mambobin ECOWAS da Asiya. Daskare duk ma'amalar sabis gami da ma'amalar makamashi. Daskare kadarorin Jamhuriyar Nijar a babban bankin Aqua. Daskarar da kadarorin jihar Neja da kamfanonin gwamnati da na kananan hukumomi a bankunan kasuwanci.

"Dakatar da ma'auni daga duk taimakon kuɗi da ma'amala tare da duk cibiyoyin kuɗi, musamman EBID", in ji shi.

Yanzu haka ana biyan dala ga daukacin 'yan Najeriya. Abokan cinikinmu suna samun kusan $5,000 - $10,000 suna samun manyan yankuna. Karanta shaidar wasu da suka amfana. Danna nan don farawa

(Daily Trust) 

Thursday, 27 July 2023

Juyin Mulkin Nijar: Ministan Bazoum Ya Nada Kansa Shugaban Gwamnati

Minitsan harkokin wajen Jamhuriyyar Nijar, Hassoumi Massoudou ya ayyana kansa a matsayin Shugaban Gwamnati, yana mai kira ga al’ummar kasar su murkushe juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Mohammed Bazoum. Kawo yanzu dai ba a san hanlin da Mista Bazoum yake ciki ba a hannun masu juyin mulkin. Amma wani sako da aka wallafa ta shafinsa na Twitter a safiyar Alhamis ya ce, “za a kare nasarar da ya samu” kuma al’ummar kasar ne za su tabbatar da hakan. Zargin kashe madugun juyin mulki? Wasu rahotanni daga kasar kuma na cewa sojojin sun kashe wanda ya jagorance su wajen yin juyin mulkin, Abdulrahman Chani. Shugaban gidan rediyon Amfani FM da ke birnin Yamai na kasar, Issoufu Mammane, ya shaida wa Aminiya cewa ana zargin an harbe shi har lahira ne a yayin takaddama kan wanda zai jagoranci gwamnatin sojin, wadda yake neman nada kansa. “A yayin jayayya saboda ya ce shi zai dauki mulki, su kuma sauran sojojin suka ce ba shi zai dauka ba ga wanda za ya dauka (Salifou Modi)… suna wannan jayayya ne wani ya ciro bindiga ya harbe shi,” a cewar Malam Issoufu Mammane. Kawo yanzu dai Aminiya ba ta iya tabbatar da faruwar hakan ba. Har yanzu dai masu juyin mulkin ba su sanar da sunan wanda zai jagoranci gwamnatin da suka kafa ba, wanda hakan ya sa ake ta hasashe. Bayan tabbatar da kifar da gwamnatin Bazoum, kakakin sojojin, Kanar Manjo Ahmadou Abdrahamane, ya kuma sanar da rufe duk iyakokin kasar da kuma hana zirga-zirga a cikin kasar daga karfe 10 na dare zuwa 7 na safe. Sojojin sun sauke daukacin ministoci daga mukamansu, don haka manyan sakataron ma’aikatun ne za su ci gaba da gudanar da su. Kannar Manjo Ahmadou Abdrahamane, ya kuma bukaci kasashen waje da kada su tsoma bakinsu a cikin wannan al’amuri na cikin gidan kasar Nijar. A cewarsa, sojojin sun kifar da gwamantin Bazoum ne saboda matsalar tsaro da karancin ababen more rayuwa da kuma koma-bayan tattalin da suka addabi kasar. A wane hali Bazoum yake? Sai dai kuma a hannu guda, minitsan harkokin waje na kasar, Hassoumi Massoudou ya ayyana kansa a matsayin Shugaban Gwamnatin kasar, yana mai kira ga al’ummar kasar da su kawo karshen juyin mulkin da sojojin kasar suka yi wa Shugaba Mohammed Bazoum. Amma kawo yanzu dai babu wani bayani game da halin da Mohamed Bazoum yake ciki a hannun sojojin da ke tsare da shi ba. Hakazalika babu bayani game da ko ya amince ya ajiye mukaminsa, ballantana na makomarsa. Yuyin mulki a yankin Sahel Yanzu Nijar ta zama kasa ta hudu a fadin yankin Sahel — wadandan dukkansu rainon Farasan ne — da baya-bayan nan sojoji suka yi juyin mulki. Kasashen Sahel da ke yankin Afirka ta Yamma (Burkina Faso, Mali, Chadi Kamaru da Nijar) masu makwabtaka da Najeriya na fama da matsalar ta’addanci da na tattalin arziki. Nijar, daya daga cikin kasashe matalauta a Afirka, na fama da matsalar masu ikirarin jihadi nau’i biyu a yankin Kudancin kasar. Yakin Kudu maso Gabas na fama da ta’addancin Boko Haram da ISWAP da ta gangaro daga Arewa maso Gabashin Najeriya. A yankin Kudu maso Yamma kuma matsalar ta gangaro ne daga kasar Mali tun shekarar 2015. Kasashe biyar na yankin (Nijar, Chadi, Mali, Burkina Faso, Mauritaniya) da Najeriya sun kafa kungiyar G5 Sahel domin yakar ta’addanci, a yayin da suke fama da masu da’awar jihadi, kamar yadda Najeriya ke fama da Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas. Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya da Fadar White House ta Amurka da Tarayyar Turai da kasar Faransa, wadda ta raini Jamhuriyar Nijar suka la’anci abin da sojojin na Nijar suka yi. Ba za mu lamunci juyin mulki ba — ECOWAS Kungiyar raya tattalin arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), wadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya yake jagoranta ta ce ba za ta lamunci karin juyin mulki a Nijar ko wata kasa a yankin ba. Tuni ECOWAS ta tura tawaga ta musamman karkashin Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyar Benin domin shiga tsakani. A ranar Alhamis ake sa ran tawagar ta ECOWAS za ta gana da bangaororin bangarorin biyu da nufin sasanta rikicin. Juyin mulki a Nijar Baya ga yunkuri da aka yi a lokuta daban-daban na kifar da gwamnati kasar, wannan shi ne karo na hudu da aka yi juyin mulki a Nijar tun bayan samun ’yancin kanta a shekarar 1960. Yunkurin juyin mulki na karshe a kasar shi ne wanda aka yi a jajibirin rantsar da Mista Bazoum a shekarar 2021. Shugaba Bazoum wanda amini ne na kut da kut da Faransa, an zabe shi ne a shekarar 2021 domin jagorantar kasar da ke fama da talauci, yayin da take da tarihin samun rashin zaman lafiya.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...