Fitaccen dan kwallon duniya, Pele ya mutu
Fitaccen ɗan ƙwallon nan na duniya ɗan ƙsar Brazil, Pele ya rasu yana da shekara 82. Pele ya rasu ne a ranar Alhamis 29 ga watan Disamban 2022 bayan ya sha fama da rashin lafiya. A kwanakin baya an yi ta yaɗa labarin ƙarya na rasuwarsa. Ya rasu ne sakamakon cutar kansar ƙaba da kuma cutar ƙoda Ana ganin Pele shi ne ɗan ƙwallon da ba a taɓa samun irin sa ba a duniya, kuma sau uku yana cin gasar kofin duniya wa ƙasarsa Brazil. Ya ci kofin duniya a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970. A shekarar 2000 ne kuma hukumar ƙwallon ƙafar duniya FIFA, ta ayyana shi a matsayin ɗan ƙwallon ƙarni. Shi ne ɗan ƙwallon da ya kafa tarihin zura ƙwallaye 1,281 a raga a cikin wasanni 1,363 cikin shekara 21 da ya yi yana buga tamaula. Cikin waɗannan har da ƙwallo 77 da ya ci wa ƙasarsa cikin wasanni 92 da ya buga wa Brazil ɗin. An yi wa Pele tiyata a kan yanke masa kansa a hanjinsa a watan Satumban 2021 a Asibitin Albert Einstein da ke Sao Paulo. An sake kwantar da shi a asibiti a watan Nuwamban 2022. Ƴ...