Matawalle ya dakatar da yakin neman zaben APC a Zamfara

Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya dakatar da yakin neman zaben Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara har zuwa ranar 18 ga watan Janairu da muke ciki.

Rohotanni sun bayyana cewa kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar ya dakatar da harkkokin kamfe din gwamnan ne don mayar sa hankali kan zaman lafiya a jihar.

“Na yi alkawarin mayar da hankali wajen dawo da zaman lafiya a mulkina na biyu a Jihar Zamfara,” cewar Matawalle.

Aminiya ta ruwaito cewa Ya bayyana haka ne a lokacin da jam’iyyar ta kaddamar da yakin neman zabensa a Karamar Hukumar Kaura Namoda, a ranar 27 ga watan Disamba, 2022.

Matawalle dai ya nada tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zabensa.

A nasa bangaren, tsohon gwamnan jihar ya ce matsalar tsaro za ta inganta idan Matawalle ya sake darewa kujerar mulkin jihar a karo na biyu.

Yari, wanda ya jagoranci kwamitin yakin neman zaben APC zuwa kamfe din jam’iyyar ya ce zai goyi bayan takarar Matawalle dari bisa dari.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki