Posts
Showing posts with the label Gwamna Ganduje
2023: Dalilin Da Ya Sa Muka Tsayar Da Gawuna Takarar Gwamnan Kano– Ganduje
- Get link
- X
- Other Apps
By Nura Ahmad
alheekmahnews.ng.com
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar sun tsayar da Mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin dan takarar Gwamnan jam’iyyar a zaben 2023 ne saboda kwarewarsa. Ya ce biyayya da ilimi da kwarewa da kuma kyakkyawar mu’amalarsa da jama’a su ne suka karfafa zaben nasa. Yana mai cewa, babu wata jam’iyya a Kano da ke da dan takara kwararre irin Gawuna. Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron gidauniyar da abokin Gawuna ya shirya a Abuja. “Dokta Gawuna na sane da shirye-shirye da kuma ayyukanmu, kuma mun yi amannar mutum ne wanda zai taimaka wa cigaban al’uma. “Wannan shi ne irin mutanen da muke raino, wadanda za su yi tsayin daka wajen ci gaba daga inda aka tsaya da kyawawan ayyukan bunkasa al’uma da aka asassa. Inshaa Allah za mu ci gaba da haka. A cewar Ganduje, “Daya daga cikin abubuwan da muka yi la’akri da su shi ne ci gaba da ayyuka saboda muhimmancin hakan a sha’anin shugabannci. “Mun tattara ba...