Mutum miliyan bakwai ne suka yi aikin Umarah a shekarar 2022- Saudia

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umarah ta kasar Saudiyya ta ce kimanin mutum miliyan bakwai ne suka yi aikin Umarah a shekarar 2022.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa wannan adadin a cewar ma’aikatar ya hada da baki su miliyan hudun da suka samu izinin shiga kasar domin Hajjin Umarah.

Kamfanin dillancin labarai na SPA ya rawaito a ranar Alhamis cewar, Ma’aikatar ta yi amfani da harsuna 14 wajen isar da muhiman bayanai da suka shafi addini da kiwon lafiya da sauransu ga maniyyatan yayin zamansu a kasar.

Kazalika, ta ce ta tabbatar da maniyyatan sun samu kulawar da ta dace wajen gudanar da harkokinsu da suka hada yanka da ziyartar wurare da sauransu.

Ta kara da cewa, ta sahale wa masu rike da biza daban-daban ibadar Umarah a wannan shekarar.

Ta ce a 2022 ne ta kyale masu bizar yawon shakatawa suka yi Umarah yayin zamansu a kasar, wanda hakan shi ne karon farko da irin hakan ta faru.


Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki