Posts

Showing posts with the label Buhari

Kotu Ta Dage Shari'ar Rarara Kan Sukar Buhari

Image
Wata Kotun Majistiri da ke zamanta a Lafiya, babban birnin Jihar Nassarawa, ta dage sauraron kara da aka shigar da mawakin siyasa, Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, kan zarginsa da neman tunzura al’umma da kuma tayar da hankali. Karar wanda wani mazaunin garin Mararraba da ke makotaka da Abuja mai suna Muhammad Sani Zangina ya shigar, ya danganta shi ne da wani jawabin taron ’yan jarida da ya ce mawakin ya shirya a Abuja, inda ya bayyana nadamar goyon bayansa ga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tare da zarginsa da wargaza kasar kafin mika ta ga Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu. An sa zare tsakanin Rarara da mutanen Buhari Sabuwar wakar Rarara ta sake yamutsa hazo A takardar karar wadda wakilinmu ya samu gani, lauyan mai shigar da karar, Barista Muhammad Barde Abdullahi ya gabatar, ya ce zargin da ake yi wa Rararan da aikatawa, ya saba da doka ta 114 a Kundin Shari’a na penal code. Sai dai a yayin zaman fara sauraron shari’ar a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba,

MARTANI GA MAWAKI DAUDA RARARA - Bashir Ahmad

Image
Na kalli wani bangare na videon da yake yawo na taron manema labarai da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gabatar a yau, musamman bangarorin da ya ci wa tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari mutunci tare da zargin cewa sai da ya rusa kasar baki daya kafin ya bar mulki.  Bayan kammala kallon video na yi yunkurin bawa Rarara amsa daya bayan daya ga duk wadannan zarge - zargen da yayi, sai dai daga bisani da na sake yin nazari a tsanake sai na ga babu bukatar hakan a halkance da kuma mutunce, saboda wasu dalilai kwarara guda biyu. Na farko, cikin videon, Rarara yayi ikirarin cewa wai gudunmawar daya bayar a tafiyar Buhari ko shi Buharin bai bawa kan sa irin wannnan gudunmawa ba. IKON ALLAH. Don Allah akwai hankali a cikin wannan magana?  Sai dalili na biyu, inda yake cewa a wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu idan har ba a bashi mukamin minista ba, to ya kamata a ce an kira shi an zauna da shi an zabi wadanda za a bawa mukaman na ministoci. TASHIN HANKALI. Ko akwai chemistry, ball

Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Fara Tashin Alhazan 2023, Inda Yay Kira Garesu Dasu Zama Jakadu Na gari

Image
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da jigilar jigilar maniyyata aikin hajjin bana. An kaddamar da jirgin na farko a ranar Alhamis a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport Abuja. Shugaban ya kaddamar da jirgin na farko da karfe 1:30 na rana Shugaban wanda Karamin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Zubairu Dada ya wakilta a wajen taron ya yabawa Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) bisa nasarar shirye-shiryen Hajjin 2023. Da yake jawabi ga hukumar ta NAHCON, Ambasada Dada ya ce "NAHCON tana yin aiki mai ban al'ajabi kuma Shugaba Buhari ya yaba da abubuwan da kuke yi tun hawan ku". Daga nan sai shugaban ya gargadi jami’an aikin Hajji da kada su yi kasa a gwiwa, amma “ku ci gaba da tafiya. Bari wannan ya zama farkon aikin wanda shine Jin dadin Alhazai. “Ka taimaka musu gwargwadon iko don ba su damar sauke nauyin da suke kansu na addini da suke can. Wasu daga cikinsu ba su taba yin balaguro a wajen al’ummarsu ba, aikinku yana nufin cewa an dam

An Sanya Wa Gadar Neja Ta 2 Da Buhari Ya Gina Sunansa

Image
An sanya wa Gadar Neja ta Biyu, wacce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gina a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ya kuma kaddamar da ita ranar Talata sunansa. Hadimin Shugaban a fannin kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad ne ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter ranar Talata. Jama’a sun kashe ‘barawon babur’, sun kone gawarsa a Gombe Buhari ya kaddamar da Titin Kano-Kaduna da Gadar Neja II A cewarsa, “Ya ku maza da mata, yanzu a hukumance ta tabbata an sanya wa gadar Neja ta Biyu sunan Muhammadu Buhari.” Kazalika, shi ma Hadimin Buharin a kafafen sada zumunta, Tolu Ogunlesi, shi ma ya tabbatar da labarin a shafin nasa na Twitter. Sai dai ya ce sanya sunan kawai zai tabbata ne bayan amincewar Gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki na yankin. “Tare da amincewar Gwamnoni da saura masu ruwa da tsakin yankin Arewa maso Gabas, yanzu za a rika kiran gadar da sunan Muhammadu Buhari,” kamar yadda ya wallafa a shafin nasa na Twitter. AMINIYA 

Ba Ni Da Gida A Kasar Waje - Buhari

Image
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba shi da gida a wajen Najeriya. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar wasikar girmamawa daga jakadan Birtaniya a Najeriya, Richard Hugh Montgomery da takwaransa na Sri Lanka Velupillai Kananathan a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis. Buhari ya ce “A daya daga cikin ganawarmu da Sarki Charles III, ya tambaye ni ko ina da gida a Ingila, amma na shaida masa cewar ba ni da gida a wajen Najeriya.” Ya kara da cewa, an shafe shekaru da yawa ana musayar al’adu ta hanyar ilimi da horarwa tare da Birtaniya, inda ya nuna cewa ya samu horon soji a makarantar Mons Officer Cadet da ke Aldershot a Ingila 1962 zuwa 1963. Buhari ya shaida wa jami’in diflomasiyyar Birtaniya cewa kyakkyawar fahimtar banbance-banbancen al’adu, da mutunta cibiyoyi shi ne ya share fagen yawan nasarorin da Birtaniya ta samu. Ya ce jami’an diflomasiyyar da suka gabata sun kulla alaka da Sarkin Musulmi, Sarkin Kano, Shehun Borno da Sarkin Ilorin. Shugaba Buhari ya kuma

Lokaci ya yi da za ku cika alkawuran yakin neman zabenku – Buhari ga zababbun gwamnoni

Image
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga sabbin gwamnonin da aka zaba a kasar nan da su cika alkawuran da suka yi wa al’ummar kasar yayin yakin neman zabe idan sun karbi mulki. Buhari ya ba da shawarar ne a cikin jawabinsa, wanda shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari ya gabatar a Abuja ranar Litinin a wurin taron kaddamar da gwamnoni, wanda kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta shirya. “A watan Maris na 2023, Najeriya ta karfafa tare da karfafa tsarin dimokuradiyyar ta tare da babban zabe wanda aka gudanar da zaben sabon shugaban kasa da kuma sabbin gwamnoni 18 da aka zaba/ masu shigowa. “Na yi farin cikin lura da cewa dimokuradiyya tana nan a raye, tana nan kuma tana ci gaba a Najeriya. "Yayin da zabe ya kare, lokaci ya yi da za mu cika alkawuran da muka yi a lokacin yakin neman zabe," in ji shi. Buhari ya ce nan da ranar 29 ga watan Mayu za a yi kira ga gwamnonin da aka zaba su tafiyar da al’amuran Jihohinsu na tsawon shekaru hudu ma

Buhari Zai Je London Bikin Nadin Sarkin Ingila

Image
A yau Shugaba Muhammadu Buhari zai yi bulaguro zuwa kasar Birtaniya domin halartar bikin nadin Sarki Charles III da matarsa Camilla. Buhari wanda zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnatinsa, yana daga ciki shugabannin duniya da Fadar Burkingham ta Birtaniya gayyata domin halartar bikin da zai gudana ranar Asabar, 6 ga watan Mayu. Daliban Najeriya da suka isa Port Sudan za su iya hawa jirgin sama Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya ce gabanin bikin nadin Sarki Charle III, Kungiyar Kasshe Rainon Ingila za ta gudanar da babban taronta a ranar Juma’a 5 ga wata. Taron, wanda Buhari zai halarta zai tattauna da kan makomar kasashen da muka rawar da matasa za su taka.

Gwamnatin Tinubu Ce Za Gudanar Da Kidaya —Buhari

Image
  Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a dage lokacin gudanar da Kidayar Jama’a da Gidaje da aka shirya farawa ranar 3 ga watan Mayu mai kamawa. Kwana hudu kafin fara aikin Buhari ya ce ya bai wa gwamnati mai jiran gado damar yanke shawara kan lokacin gudanar da kidayar domin tabbatar da nasararsa. Ya sake dage lokacin gudanar da kidayar ne bayan wata ganawa da tsakanin Shugaba Buhari da shugaban hukumar, Nasir Isa Kwarra tare da Majalisar Zartarwa ta Tarayya a ranar Juma’a a Fadar Shugaban Kasa. Sanarwar da Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed ya fitar ta ce duk da haka Shugaba Buhari ya jaddada muhimmancin gudanar da kidayar wadda rabon da a gudanar shekara 17 ke nan. Shugaban ya kuma yaba da kyakkyawatan shirin da hukumar ta yi wa kidayar, wanda zai tabbatar da ingancinsa kamar na sauran kasashen duniya. Wata majiya a hukumar ta ce an dage aikin kidayar ne saboda wasu matsalolin da hukumar ke fuskanta da za su hana ta gudanar da aikin a lokaci guda; sai dai ba ta yi kari

Labari da dumiduminsa : Shugaba Buhari Ya Dage Kidayar 2023

Image
A wata ganawa da ya yi da mambobin majalisar zartaswa ta tarayya da kuma shugaban hukumar kidaya ta kasa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023, wadda aka shirya gudanarwa tun daga ranar 3-7 ga watan Mayun 2023. Za a tantance sabon ranar ne ta hanyar gwamnati mai shigowa. An cimma matsayar ne bayan taron ya jaddada muhimmancin da ke akwai na kidayar jama’a, wanda ba a yi ta tsawon shekaru 17 ba, na tattara sabbin bayanai domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, da kuma fitar da manufofin ci gaban kasar. Duk da irin gagarumin ci gaban da aka samu da suka hada da kammala aikin tantance yankin da kuma daukar ma'aikata da horar da ma'aikata, shugaban ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati mai jiran gado ta samu damar karfafa wadannan nasarori. Shugaba Buhari ya yaba wa tsarin hukumar kidaya ta kasa, musamman yadda ake tura na’urorin zamani domin tabbatar da kidayar jama’a mai inganci kuma abin dogaro. An umurci hukum

PDP Ta Bukaci Sanyawa Buhari Takunkumi

Image
Babbar jam’iyyar adawar Najeriya ta PDP ta bukaci kasashen duniya da su hana shugaban kasa Muhammadu Buhari bizar tafiye tafiye da zaran ya mika mulki ranar 29 ga watan gobe, saboda abinda ta kira kalamansa dangane da zaben shugaban kasar da akayi ranar 25 ga watan Fabarairu.  Yayin tsokaci akan zaben, Buhari ya bayyana ‘yan adawar Najeriya a matsayin wadanda suka shantake akan cewar zasu samu nasara ba tare da neman goyan bayan jama’a kamar yadda jam’iyarsa ta APC tayi ba.  Sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar Debo Ologunagba yace kalaman shugaban na iya tinzira jama’a da kuma haifar da illa ga zaman lafiyar kasar.  Ologunagba ya kuma ce kalaman na iya karfafawa alkalai gwuiwa wajen yanke hukunci akan karar da suka shigar a gaban kotu domin kalubalantar sakamakon zaben wanda yace tuni wasu a ciki da wajen kasar ke bayyana shi a matsayin mafi muni a tarihin Najeriya.  Jam’iyyar PDP tace zaben da akayi bana ya gamu da matsalolin da suka sabawa kundin tsarin mulkin kasa da

Ci-da-zucin 'yan adawa ne ya kayar da su zaɓe - Buhari

Image
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya yi imani ci-da-zuci ne babban abin da ya janyo taron 'yan adawar Najeriya suka sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa da ya wuce. Ya bayyana haka lokacin da ya karɓi gwamnonin jam'iyyarsa ta APC a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi. Yana cewa a daidai lokacin da jam'iyya mai mulki take aiki tuƙuru don ci gaba da mulki a zaɓukan da aka yi a baya-bayan nan, 'yan adawa suna can sun cika da ci-da-zuci. "Sun je suna ta faɗa wa masu goya musu baya a ƙasashen waje cewa, sai sun kayar da APC. Yayin zaɓen na 25 ga watan Fabrairu, ɗan takarar jam'iyyar APC mai mulki Bola Ahmed Tinubu ya smau ƙuri'a 8,794,726. Sai Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya samu ƙuri'a miliyan 6,984,520. Ɗan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi yana da ƙuri'a miliyan 6,101,533, yayin da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya zo na hudu da ƙuri'a miliyan 1,496,687. Shugaba Bu

Buhari Ya Je Wurin Fareti Sanye Da Kakin Soja

Image
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito sanye da kakin sojoji a dandalin Eagles Square inda sojoji ke fareti a safiyar Alhamis.  Buhari ya isa dandalin, inda sojoji 1,000 ke gabatar da fareti inda ya samu rakiyar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari. Babban Hafsan Taron Najeriya, Janar Lukcy Irabor da Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Faruk Yahaya da kuma Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba na daga cikin mahalarta faretin. Sauran hafsoshin tsaro da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan na daga cikin mahalarta faretin sojojin. AMINIYA

Buhari Zai Bar Najeriya Fiye Da Yadda Ya Same Ta – Fadar Shugaban Kasa

Image
  Fadar Shugaban Kasa ta ce a fannin tsaro da habaka tattalin arziki, Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015. Kakakin Shugaban, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels ranar Talata. Ya kuma ce karyata batun cewa a tsawon mulkin Buhari na shekara takwas, ya nuna kabilanci wajen nafin wadanda za su shugabanci hukumomin tsaron kasar nan. A cewarsa, nadin nasu ba shi da wata alaka da addinin, yanki ko kabilar da mutum ya fito wajen nadinsu, an fi la’akari da cancanta tun da dai doka ta ba Shugaban ikon nada duk wanda ya ga dama. Dangane da batun cewa an fi kashe mutane masu yawa a mulkin Buhari fiye da a shekarun baya duk da cewa bangaren tsaro na cikin manyan abubuwan da ya yi alakawari a kansu, Femi Adesina ya ce ba gaskiya ba ne. Ya ce, “Ka san cewa akwai wani rahoto da ya ce an fi samun karancin mutanen da aka kashe a 2022 a cikin shekara 12 da suka gabata a sakamakon ayyukan ta’addanci? Mun fa sani

Rashin Lafiyar Buhari Ta Kawo Wa Gwamnatinsa Cikas —Adesina

Image
Mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce rashin lafiyar da Shugaban Kasa ya yi a 2017 ta janyo wa gwamnatinsa nakasun aiki na watanni takwas a mulkinsa. Adesina ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake zanta wa a gidan talabijin na Channels. Adesina, wanda ya bayyana nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a yayin zantawar, ya ce shugaban ya shafe watanni takwas yana jinya a Ingila a 2017. “Lokacin da ya soma rashin lafiya a watan Janairun 2017, ya dawo a watan Maris, ya sake komawa a watan Afrilu kuma bai dawo ba sai 19 ga watan Agusta. “Wannan jinya ta dauki wata takwas ba tare da yana aiwatar da komai ba. Tabbas, babu wanda zai so hakan amma abun farin ciki shi ne daga baya ya samu lafiya.” Sai dai ya ce duk da wannan koma baya da aka samu, shugaba Buhari zai bar kasar nan cikin nagarta fiye da yadda ya same ta. Adesina ya bayyana cewa a shekarar 2015 lokacin da Buhari ya karbi mulki, kananan hukumomi 1

Labari Da dumiduminsa: Buhari Ya Tafi Kasar Saudiyya A Ziyarar Karshe A Matsayin Shugaban Kasa

Image
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Saudiyya a ziyarar aiki daga ranar Talata 11 zuwa 19 ga watan Afrilu a ziyararsa ta karshe a matsayinsa na shugaban kasa, inda zai gudanar da aikin Umrah, karamar hukumar. Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban ya bi sahun sauran masu ibada a fadar gwamnati da ke Abuja, domin ganin an rufe tafsirin Alkur’ani na yau da kullum, saboda ziyarar da Limamin zai yi na Umrah zuwa Saudiyya. Shehu ya ce karatun kur’ani da tafsirin wani abu ne na yau da kullum na azumin watan Ramadan a wuraren ibadar musulmi kuma na bana yana da ma’ana ta musamman ga shugaban. Ya ce ranar Juma’ar da ta gabata ita ce karo na karshe da zai gudanar da tafsirin a matsayin shugaban kasa kuma babban kwamandan rundunar tare da la’akari da ranar mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu. Shehu ya ce a yayin da Shuga

Shugaba Buhari Yace, Bai Umarci Atoni Janar Da Gwamnan CBN Kan Kin Bin Umarnin Kotu Ba Dangane Batun Tsofaffin Kudi

Image
  Fadar shugaban kasa na son mayar da martani kan wasu damuwar da jama’a ke ciki na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai mayar da martani ga hukuncin da kotun koli ta yanke kan batun kudin tsohon naira 500 da naira 1,000 ba, kuma ta bayyana a nan karara da cewa babu wani lokaci da ya umurci Babban Lauyan gwamnati da Gwamnan CBN su bijirewa duk wani umarnin kotu da ya shafi gwamnati da sauran bangarorin. A sanarwar da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce, tunda aka rantsar da shugaban kasa a shekarar 2015, bai taba umurtar kowa da ya bijirewa umarnin kotu ba, bisa akidar cewa ba za mu iya gudanar da mulkin dimokuradiyya ba tare da bin doka da oda ba, kuma jajircewar gwamnatinsa kan wannan ka’ida ba ta canja ba. Bayan zazzafar muhawarar da ake ta yi game da bin doka da oda dangane da halaccin tsohon takardun kudin, don haka fadar shugaban kasar na son bayyana karara cewa Shugaba Buhari bai yi wani abu da

Buhari Ya Je Maiduguri Domin Jajantawa 'Yan Kasuwar Monday Market

Image
Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari ya isa Jihar Borno, domin jajanta wa ’yan kasuwar da iftila’in gobora ta shafa a Kasuwar Monday da ke Maiduguri. An wayi gari ranar Lahadi a Maiduguri da gobarar, wadda ta lakume dubban shaguna a kasuwar, wadda ita ce mafi girma a Jihar Borno da ma yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. ’Yan sanda na ci gaba da tsare Ali Madaki kan daukar bindiga a yakin neman zabe Ana sa ran a yayin ziyarar ta ranar Alhamis, Buhari zai je Fadar Shehun Borno, inda zai jajanta wa ’yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyinsu a gobarar ta ranar Lahadi. Shugaban kasar zai kuma kaddamar wa wasu ayyuka da suka hada da rukunin gidajen da Gwamna Babagana Zulum ya gina da wasu tituna a garin Maiduguri. Sauran su ne Cibiyar Kula da Masu Cutar Kansa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da kuma Tashar Iskar Gas ta kamfanin NNPC.

Bankin CBN Ya ce Har Yau Yana Nan Kan Bin Umarnin Shugaba Buhari Na Ci Gaba Da Amafani Da Tsofaffin Kudi Na 200 Kadai

Image

APC Ta Bukaci Buhari Ya Mutunta Umarnin Kotun Koli Kan Wa’adin Tsofaffin Kudi

Image
Kwamitin Gudanarwar APC na kasa ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari da ya martaba hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan batun daina amfani da tsofaffin takardun kudi. Wannan kira dai na zuwa ne yayin wani taro da gwamnonin jam’iyyar da shugabanta na kasa, Sanata Abdullahi Adamu suka gudanar ranar Lahadi a Abuja. NAJERIYA A YAU: Shin don talakawa gwamnoni ke adawa da canjin kudi? Tsohon Shugaban PDP a Kano ya sauya sheka zuwa NNPP A taron wanda aka shafe tsawon sa’a biya ana tattaunawa, ya kara nuna yadda APC ta tsunduma cikin rudani da rabuwar kawuna, inda shugabancin jam’iyyar ya bi sahun wasu gwamnonin kasar da ke fito-na-fito da manufar daina karbar tsoffin kudi ta Shugaba Buhari. A cewar Kwamitin, “Muna kira ga Babban Ministan Shari’a na Tarayya da Gwamnan Babban Bankin Najeriya da su mutunta umarnin Kotun Koli na wucin gadi wanda har yanzu ke gabanta. “Taron yana kira ga Shugaba Buhari da ya sa baki wajen warware matsalolin da canjin kudin ya haifar wa ‘yan Najeriya.” A h

Buhari Ya Ce A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Takardun N200

Image
  Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarni a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira 200. Buhari ya ba da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin N200 ne ga Babban Bankin Najeriya (CBN) a yayin jawabinsa ga ‘yan Najeriya a safiyar Alhamis. Ya kara wa’adin amfani da tsoffin takardun N200 ne da kwana 60 zuwa ranar 20 ga watan Afrilu, 2023. Hakan na zuwa ne washegarin da Kotun Koli ta dage sauraron karar da wasu gwamnatocin  jihohi suka shigar na kalubalantar dokar haramta amfani da tsoffin N1,000 da N500 da kuna N200 da CBN ta canja.