Wasu Daga Yan Asalin Kiru Da Bebeji Da Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Samawa Ayyukan Gwamnati
WASU DAGA CIKIN OFFER TA AIKI MAI FANSHO A GWAMNATIN TARAYYA DA HON ABDULMUMIN JIBRIN KOFA YA SAMAR WA ’YAN ASALIN KIRU/BEBEJI, KANO KAFIN HAWANSA NA HUDU A MAJALISAR WAKILAI Idan za a iya tunawa, Hon Abdulmumin Jibrin Kofa, ya yi shekaru huɗu (2011-2015) a wa’adin mulkinsa na farko, sai kuma ƙasa da shekaru biyu (2015-2016) da kuma (2018-2019) a wa’adi na biyu, sai kuma watanni shida kacal (2019-Jan 2020) a wa’adinsa na uku. Yanzu kuma a wa’adinsa na huɗu da yake kai, shekara ɗaya ke nan da ɗoriya (2023-2024). A sanarwar da hadimin Dan Majalisar kan Harkokin yada labarai, Sani Ibrahim Paki ya sanyawa hannu, yace amma duk da haka, ya yi namijin ƙoƙari wajen samar wa matasa masu matsayin karatun digiri, HND, difloma da ma sakandare ayyukan yi a matakin gwamnatin tarayya. Tuni wasu daga cikin waɗannan mutanen suka fara yin girma a wuraren ayyukan nasu kuma sun samu rufin asiri suna ci gaba da ɗaukar nauyin iyalai da ’yan uwansu da jamaa da kuma mazabu da yank...