Posts

Showing posts with the label Motar Haya

Gamu Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na 4- Dr Dukawa

Image
HALIN DA TITUNAN NAJERIYA SUKE CIKI Tafiyar da muka yi daga Kano zuwa Yola ta dauke mu kimanin awa tara (9.30 na safe – 6.30 na yamma). Kuma na yaba da tukin direbanmu, wani matashi mai suna Uzairu dan kimanin shekara 25/6. Wannan tafiyar ta tuna min da wani majigi da shahararren masanin kimiyar siyasa, Farfesa Ali Mazrui, ya yi a shekarun 1980. Ali Mazrui dan asalin Kenya ne, ya auri ‘yar Najeriya, sun rayu a America har rasuwarsa.  Guda daga cikin hanyoyin da Ali Mazrui ya bi wajen nuna tazarar da take tsaknin manyan kasashe da masu tasowa shine yadda ya dauko hoton wani titi a wata babbar kasa (watakil America) da motoci suna gudu kowacce a layinta. Sai ya ce: “duk wanda ka gani yana tuki yana kwane-kwane anan, to a cikin maye yake”. Sai kuma ya dauko wani titi na wata kasar mai tasowa (watakila Kenya ko Najeriya), da motoci suna ta kwane-kwane suna kaucewa ramukan kan titi. Sai ya ce: “anan kuma, duk wanda ka gani yana tafiya sambel babu kwane-kwane to a buge yake!”  Ya

Game Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na 3 - Dr Dukawa

Image
HALIN DA WASU TASHOSHIN MOTA SUKE CIKI  A bisa kiyasi, tashar Na’ibawa a Kano ba za ta gaza shekara arba’in (40) ba. Saboda an samar da ita ne a zamanin marigayi gwamnan tsohuwar jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi (1979 – 1983). Amman har izuwa yau tashar tananan jiya ya yau: kango wanda babu wani abu da yake nuna ana samun kudi a wurin; babu kwalta, babu interlocks, babu dabe kowane iri! Zaiyar kasa. Sai yalwar leda da sauran nau’i na shara. Babu wani lafiyayyen makewayi. Da na bukaci wurin yin bawali sai aka nuna min wani uban juji a yammacin cikin tashar. Sai da roki wani dan bola jari cewar ya dan kauce zan kama ruwa.  Na tabbatar idan ruwa ya sauka mummunan halin da tashar ke ciki ba zai gaza na tashar Unguwa Uku ta Kano ba, wacce na yi rubutu akan nata halin da take ciki a sherarar 2020.  An yayyanka pilotai a cikin tashar Na’ibawa. Wasu an gina shaguna ana gudanar da ciniki wasu kuma an saka fandisho na gini ba a yi ginin ba. Babu Masallaci sai ‘yar musalla amman har da

Game Da Tafiya A Motar Haya Kashi Na Biyu

Image
  Daga Dr Sa'idu Ahmad Dukawa TSARIN DAUKAR FASINJA A TASHA Bayan da na yi tambayi game da tsarin daukar fasinja a tashar mota, na sami bayanin cewa mutum zai iya zuwa tsahar Na’ibawa (wacce a yanzu aka sakawa suna “tashar Kano Line”) ya yi booking (biyan kudi kafin ranar tafiya). Don haka sai na je ofishin Adamawa Sunshine (wanda alal hakika shago ne a cikin tashar da dan teburi da mutumin da yake karbar kudi ya rubuta rasiti), na biya kudina ana kashegarin ranar tafiya. Na tambaya mutum nawa ake dauka a mota kirar sienna? Aka ce min ana daukar mutum takwas ne, fasinja biyu a gaba, uku a tsakiya, uku a karshe. Amman fa Bature ya yi motar ne domin daukar fasinja biyar: guda a gaba, biyu a tsakiya, biyu a karshe. Don haka ana wuce kima (overload) na mutum uku. A motar ‘yankasuwa kuwa har mutum hudu ake sakawa a tsakiya, kamar yadda na ganewa idona a yayin dawowata daga Jalingo zuwa Kano. Allah ya kiyaye, a duk lokacin da aka gamu da hadari, za ta yiwu a yi asarar rayuka tara zuwa go

Game Da Tafiya Da Motar Haya A Najeriya Kashi Na Daya

Image
Daga  Dr. Saidu Ahmad Dukawa SHIMFIDA A ranar Talata, 25/4/2023, na shiga motar haya daga Kano zuwa Yola, babban birnin jihar Adamawa a Najeriya. Ranar Alhamis kuma, 27/4/23, na shiga wata motar hayar daga Yola zuwa Jalingo, babban birnin jihar Taraba. Rabona da tafiyar motar haya wacce ta kai tsawan haka tun a shekarun 1983 zuwa 1984 a yayin da na yi hidimar Kasa (NYSC) daga jihar Kano zuwa jihar Bauchi, sai kuma jihar Lagos da na je bayan kammala hidimar kasa a wajejen shekarar 1985. A wannan karon ma tafiyar ta taso min ne a dalilin wata hidimar Kasar, watau aikin kula da yadda jarrabawar shiga jami’o’i ta kasa (UTME) take gudana. Tun daga lokacin da aka nada Farfesa Is’haq Oloyede a matsayin Magatakardar Hukuma mai tsarawa da gudanar da jarrabawa domin shiga jami’a a Najeriya (JAMB), a shekarar 2016, ya fitar da sababbin tsare-tsare na yadda ake gudanar da wannan jarrabawar. Daga ciki akwai samar da kwamitoci daban daban, har guda goma sha daya (11), domin gudanar da ay