Dalilin Da Dokar Hana Lefe Ba Za Ta Yi Aiki Ba A Kano
Shi kansa mai laifi ne, domin ya yi lefe a nasa auren da na ’yan uwansa. Masani a bangaren Shari’a Barista Isa Umar Sulaiman, ya bayyana cewa duk da cewa akwai Dokar Hana Lefe a Kundin Dokokin Jihar Kano, hakan ba zai sa ta yi aiki ba saboda tana kunshe da wasu sharuÉ—a. Barista Sulaiman ya faÉ—i haka ne yayin da yake mayar da martani ga fitaccen lauyan nan da ya yi shuhura a kafafen sada zumunta, Barista Abba Hikima. A cewar Barista Sulaiman, neman tayar da kura ko kawo hargitsi ya sanya Barista Hikima ya dago da batun dokar hana lefe a jihar ta Kano. A makon da muke ciki ne dai cikin wani shiri na gidan rediyo a Jihar Kano da kuma shafinsa na Facebook, Abba Hikiman ya dauko batun cewa a Dokar Kano laifi ne ka yi lefe kamar yadda ake yi a yanzu. Wannan magana dai ta ta da kura musamman a soshiyal midiya, inda wasu ke ganin bakinsa wasu kuma ke sam barka. Sai dai Lauya Sulaiman ya ce Hikima tsakuro sashi na 5 na dokar ya yi, ba wai gaba É—aya dokar kacokan ya fassara ba. “SaÉ—arar da...