Gwamnatin Kano za ta hada gwiwa da Jami’o’i masu zaman kansu don bunkasa ci gaban dan Adam – Gwamna Abba Kabir
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce jihar za ta hada hannu da manyan jami'o'i masu zaman kansu a ciki da wajen kasar nan domin ci gaban bil'adama. A sanarwar da babban sakataren Yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, tace Gwamnan ya bayyana hakan a gidan gwamnatin Kano a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar jami’o’in Afirka masu zaman kansu Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo. Mai Martaba Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana Farfesa Gwarzo a matsayin hamshakin dan kasuwa a fannin ilimi wanda kuma ke kokarin inganta makarantun gaba da sakandare duk da karancin jarin da yake samu. Gwamnan wanda ya yaba da kokarin Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo a kokarinsa na samar da ilimin jami’a mai zaman kansa a farashi mai rahusa, ya mika hanunsa da jami’o’in jihar Kano guda biyu. Tun da farko, Farfesa Gwarzo ya ce ya ziyarci gwamnan da mataimakinsa ne domin gabatar da takardar shaidar wasu jami’o’i masu zaman kansu guda biyu da ya sa...