Posts

Showing posts with the label Kwanaki 100

Shugaban Hukumar NAHCON Ya Bayyana Cigaban Da Ya Samar Cikin Kwanaki 100, Ya Bukaci Maniyyata Su Ba Da Hadin Kai – Daga Nura Ahmad Dakata

Image
Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana muhimman nasarorin da hukumar ta samu a karkashin jagorancinsa a cikin kwanaki 100 na farkon jagorancinsa   A wata tattaunawa ta musamman da wakilinmu a Kano Farfesa Sale Usman, ya jaddada muhimmancin koyi da shugabancin da ya gabata, inda ya ce, “A rayuwa duk wanda ya riga ka mulki, ko ya yi kura-kurai, ko ya yi nasara, sai ka yi addu’a Allah ya karba nasa ayyukan alheri kuma ya gafarta masa kurakuransa. Muna yin iya kokarinmu a yanzu kuma muna addu’ar Allah Ya taimakemu mu ci gaba da tafiya kan hanya madaidaiciya”.   Ya kuma bayyana cewa shugabancinsa yana daukar darasi daga ayyukan magabata, da amfani da nasarorin da suka samu da kuma gujewa kura-kuransu.   Da yake yin tsokaci kan hakan, ya ce, “A cikin kwanaki 100 da muka yi muna shugabanci, mun cimma yarjejeniya da kamfanonin jiragen sama na rage farashin tikitin jirgin sama idan aka kwatanta da wanda aka biya a bara. ...

Taya Murnar Cika Kwanaki 100 Na Gwamna Abba Kabir Yusuf - Laminu Rabi'u Danbaffa

Image
Daga Laminu Rabi'u Danbaffa Darakta Janar Na Hukumar Alhazan Kano  Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da ya bani damar taya gwamnatin NNPP karkashin jagorancin mai girma gwamnan jihar Kano Alh, Abba Kabir Yusif murnar cika kwanaki dari a kan karagar mulki.  Hakazalika, muna taya daukacin al’ummar Jihar Kano murnar samun gwamnati mai mai da hankali kan inganta rayuwarsu ta hanyar gudanar da ayyukan raya kasa a fannonin Ilimi, Noma, Kasuwanci, Lafiya, Muhalli. Kasuwanci da wuraren sake ƙirƙira. Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha na tare da ku musamman tallafin kudi da yabawa kan hanya da kuma yadda hukumar ta gudanar da ayyukan Hajji na 2023 wanda ya samu gagarumar nasara duk da rashin jituwar da aka gada daga tsohuwar Gwamnati.      A daidai wannan lokaci, yana da kyau mu gane irin namijin kokarin da Mambobin hukumar mu karkashin jagorancin Alh, Yusif Lawan suka yi wajen karbar yabo  daga bangarori daban-daban na rayuwa bisa la'akari da y...