Posts

Showing posts with the label Yakin neman zabe

Hukumar 'Yan Sanda Ta Kano, Ta Tsare Zababben Dan Majalisar Tarayya, Ali Madaki Bisa Fitowa Da Bindiga A Yayin Yakin Neman Zabe

Image
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tsare wani zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Dala ta jihar Kano a karkashin jam’iyyar New Nigerian Peoples Party, NNPP, Aliyu Madaki. DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa Mista Madaki ya karrama wata gayyata da ‘yan sanda suka yi masa a ranar Larabar da ta gabata bayan hotonsa na bidiyo yana dauke da bindigar famfo a lokacin wani gangamin dawowa gida na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana a yanar gizo. Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa wasu ‘yan daba sun kai hari kan ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a kan titin Zaria, Kano a ranar 23 ga watan Fabrairu a babban taron yakin neman zabensa na shugaban kasa, kuma ana zargin Mista Madaki ya jagoranci murkushe barayin. Lamarin ya kai ga cafke shugabannin jam’iyyar APC mai mulki na kananan hukumomin Ungogo da Rimingado a jihar Kano, Abdullahi Ramat da Munir Dahiru da bindigu da jami’an tsaro na hadin gwiwa suka yi. Dag

Yau Ake Rufe Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Image
  Daga karfe 12 na daren yau Alhamis 23 ga Fabrairu, 2023, za a fure yakin neman zaben ’yan takarar shugaban kasa da Majalisun Tarayya da za a gudanar ranar Asabar. Dokar Zaben Najeriya ta haramta yin duk wani nau’in yakin neman zabe ko tallata dan takara daga sa’a 24 kafin ranar zabe. A yayin rubuta wannan rahoton, kusan awa 12 ya rage wa daukacin jam’iyyu da ’yan takara su yi duk abin da za su iya, su kuma rufe yakin neman zabensu, sannan a fafata a akwatunan zabe a ranar Asabar. Jam’iyyu 18 ne ke zawarcin kujerar shugaban kasa bayan kammala wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari na biyu a ranar 29 ga watan Mayu. Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa za a gudanar da zabukan ne a mazabu 1,491 da ke kananan hukumomi 774 da ke jimillar rumufunan zabe 176, 846. ’Yan Najeriya ne za su yi alkalanci a zaben mai mutum miliyan 95.5 da suka yanki katin zabe, wadanda akasarinsu matasa ne, masu shekara 18 zuwa 35, ko da yake kawo yanzu babu alkaluman adadin wadanda suka karbi katin zabensu. Many