Hajj 2024: Kungiyar fafaren hula ta bayyana damuwa kan jinkirin shirye-shiryen aikin Haji
Kungiyar (Independent Hajj Reporters) sun nuna damuwarsu kan yadda hukumomin Najeriya ke tafiyar hawainiya dangane da shirye-shiryen Hajjin 2024. Kungiyar farar hula ta ce ma'aikatar aikin hajji da umrah ta kasar Saudiyya ta bayyanawa dukkanin kasashen da suka halarci aikin Hajji tun kafin a gama aikin Hajjin 2023 cewa an fara shirye-shiryen Hajjin 2024. Ma'aikatar ta kuma sanar da mafi yawan kasashe adadin aikin Hajjin su da kuma sabbin tsare-tsare na aikin Hajjin badi. Musamman ma, ma'aikatar ta ce za a kammala dukkan ayyukan Hajji a kalla kwanaki 45 kafin Hajjin 2024 saboda za a rufe tashar bayar da biza a wannan ranar. Wannan, a cewar IHR a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin mai dauke da sa hannun kodinetan hukumar na kasa, Ibrahim Mohammed, na nufin cewa Najeriya na da kimanin watanni 4 kafin ta kammala yin dukkan shirye-shiryen da suka wajaba kamar tattarawa da ajiye kudin maniyyata, sanya hannu kan yarjejeniyar MOU da hulda da masu samar da hi