Posts

Showing posts with the label Kudin Aikin Hajji

Dalilan Da Suka Sanya Aka Samu Farashin Aikin Hajji Daban-daban Ga Jahohin Najeriya - NAHCON

Image
Tun bayan sanar da fara biyan kudin hajjin karshe ga maniyyatan Najeriya, shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) Alh. Zikrullah Kunle Hassan, a ranar Juma’ar da ta gabata, mutane daban-daban sun yi ta yin wasu tambayoyi kan dalilin da ya sa alhazan jihar za su biya kudin jirgi daban-daban daga kasa daya. Sama da watanni biyu hukumar ta yi ta kokarin ganin cewa farashin kudin bai tashi ba a tsakanin musulmin Najeriya, musamman a kan koma bayan tattalin arzikin duniya, da hauhawar farashin kayayyaki, da faduwar darajar Naira kan dala a kasuwannin duniya. kasuwar forex.  Hukumar ta samu nasarar rage farashin kasa da Naira Miliyan 3 bisa ga dukkan alamu. A lokacin da aka fara tantance kamfanonin jiragen sama don aikin Hajjin bana, Hukumar ta hannun Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta sanar da cewa tikitin tafiye-tafiyen jiragen sama ciki har da na hayar da masu jigilar alhazan ke karba yana tasiri ne da nisan da jirgin ya yi. Dalilin da ya sa tikit...

#Hajj2023: Labari Da Dumiduminsa; Hukumar NAHCON Ta Sanar Da Kudin Kujerar Aikin Hajin Bana

Image
  Shugaban Hukumar, Alhaji Zikirulla Kunle Hassan ne ya sanarwa manema labarai hakan, a yayin wani kwarkwaryar taron da hukumar ta gudanar da shugabannin hukumomin alhazai na jahohin Najeriya wanda ya gudana a ranar Juma'a Zikirulla yace karin kudin kujerar aikin Hajin na 2023 ya faru ne sakamakon tashin farashin canjin Dalar Amurka da kuma wasu inganta ayyukan kula da alhazai ta hukumomin Saudi Arabia suka yi Shugaban ya kuma sanr da ranar 21 ga watan Afurilu a matsayin ranar karshe da hukumomin da abun ya shafa zasu sanyawa hukumar aikin hajin ta kasa kudaden Maniyyatan da zasu ta shi a jahohinsu ko kuma kamfanoninsu Da yake warware yadda biyan kudaden zai kasance tsakanin shiyyoyi ko jahohin Najeriya, Kunle ya ce Jahohin dake yankin Arewa maniyyatansu zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da sha tara (2,900,19,000.00)  Sai kuma jahohin da zasu tashi ta jahohin Maiduri da Yola, su kuma maniyyatan zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari takwas da casa'in ( 2,890,00...

Hajjin Bana: Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Yi Kira Ga Maniyyata Aikin Hajin Bana, Da Su Cika Kudinsu Ya Kai Miliyan Biyu Da Dubu Dari Diya

Image
Sakaaren zartarwa na hukumar, Ambasada Muhammad Abba Danbatta ne, yayi wannan kiran a ranar Asabar cikin wata sanarwa da ya bayar. Danbatta yace tun a ranar 28 ga watan da ya gabata ne wa’adin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta bayar ga hukumomin kula da jin dadin alhazai na jahohi, na cika kudaden adadin kujerun da aka basu ya kare, inda suka nemi alfarmar kara wa’adi domin bawa maniyyatan dama “Bayan sanya hannu kan yarjejeniya ta gudanar da aikin Hajjin 2023 ta umarci jahohi da su kai a kalla daga miliyan daya da dubu dari biyar zuwa sama” Sakataren zartarwar wanda ya bayyana cewa tun a kwanakin baya, bayan da suka dawo daga kasa Indonesiya wajen taron masu ruwa da tsaki kan harkokin aikin Hajji na kasa da kasa, yace a lokacin hukumomi sun fito da sababbin dokoki wanda aka umarci hukumomin alhazai na johohi su fadawa maniyyatansu dasu cika kudinsu ya kai naira miliyan biyu da dubu dari biyar kafin a ayyana kudin kujerar “Wannan ne ya sa muke kira ga maniyyata...