Posts

Showing posts with the label Kidayar 2023

Labari da dumiduminsa : Shugaba Buhari Ya Dage Kidayar 2023

Image
A wata ganawa da ya yi da mambobin majalisar zartaswa ta tarayya da kuma shugaban hukumar kidaya ta kasa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023, wadda aka shirya gudanarwa tun daga ranar 3-7 ga watan Mayun 2023. Za a tantance sabon ranar ne ta hanyar gwamnati mai shigowa. An cimma matsayar ne bayan taron ya jaddada muhimmancin da ke akwai na kidayar jama’a, wanda ba a yi ta tsawon shekaru 17 ba, na tattara sabbin bayanai domin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, da kuma fitar da manufofin ci gaban kasar. Duk da irin gagarumin ci gaban da aka samu da suka hada da kammala aikin tantance yankin da kuma daukar ma'aikata da horar da ma'aikata, shugaban ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati mai jiran gado ta samu damar karfafa wadannan nasarori. Shugaba Buhari ya yaba wa tsarin hukumar kidaya ta kasa, musamman yadda ake tura na’urorin zamani domin tabbatar da kidayar jama’a mai inganci kuma abin dogaro. An umurci hukum...