Posts

Showing posts with the label CI gaban Arewa

Gwamnonin Arewa maso Yamma sun tsara hanyoyin da za a bi don ci gaban yankin

Image
A kokarin samar da ci gaba mai dorewa da wadata tattalin arziki, gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun amince su hada kai da juna domin amfanin yankin. A sanarwar da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, yace Gwamnonin sun bayyana hakan ne bayan wani taro da suka gudanar a yau (Talata) a gidan gwamnatin Katsina da ke jihar Katsina. Taron wanda ya samu halartar gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, gwamnan jihar Zamfara Alhaji Dauda Lawal, gwamnan jihar Kebbi H.E. Kauran Gwandu, Gwamnan jihar Sokoto Alh. Ahmed Aliyu, gwamnan jihar Jigawa wanda ya samu wakilcin mataimakinsa da gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umaru Radda wanda ya kasance mai masaukin baki. Yayin da suke jawabi ga manema labarai na hadin gwiwa jim kadan bayan kammala taron, gwamnonin sun amince da samar da wata manufa guda domin tinkarar kalubalen tsaro da ya addabi yankin a shekarun baya. Haka kuma an amince da yin aiki tare wajen inganta fannin noma ta hany...