Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu - Abdallah Amdaz
Daga Abdallah Amdaz Alhamdulillah, Dalilin da ya saka zanyi magana akan wannan bawan Allah wanda ko saninsa banyi ba shi ne, saboda ya burgeni sosai matuƙa, ma sha Allah gashi matashi, ga karsashi Mallam abun gwanin ban sha'awa, wallahi ni ko sunansa ma ban sani ba, kuma ban damu da in sani ba, kawai dai ko ina yake a faɗin duniya, idan ya samu saƙona ina shaida masa cewa, YAYI DAI-DAI, yaci gaba a haka ake zama abun kwatance a duniya, domin juma'ar da zatai kyau tun daga Laraba ake gane ta. Abun takaicin shi ne adawa da kin gaskiya da kokarin tozarta dan Adam ya rufewa mutane idanun, suna aibata shi saboda son zuciya, don kawai suna da banbancin jam'iyya, wannan kuskure ne babba, kasarmu da al'ummar mu sune a gaban kowa, in kaga munyi fada dakai kaci mutuncinsu ne, koka danne hakkin su. Sannan ni Abdallah Amdaz ba yaron kowanne dan siyasa bane, kuma niba karan kowa bane da zaisani nayiwa wanda baya so haushi, ra'ayin kaina kawai nakeyi, don haka inkaga ...