Search This Blog

Showing posts with label Zagon Kasa. Show all posts
Showing posts with label Zagon Kasa. Show all posts

Saturday, 29 April 2023

Ba Ma Yi Wa Shirin Mika Mulki Zagon Kasa - Ganduje

Gwamnatin jihar Kano  ta ce a shirye take domin miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin ruwan sanyi ba tare da tayar da ƙura ba.

Cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai Muhammad Garba, gwamnatin ta ce tuni aka samar da babban kwamiti da kuma ƙanana da za su taimaka domin ganin an miƙa mulkin salin alin.

Ya musanta iƙirarin jam’iyyar NNPP da ta ke jiran karɓar mulki na cewa gwamnatin Ganduje na yi wa shirin miƙa mulki zagon ƙasa.

Kwamishinan ya ƙara da cewa kwamitin miƙa mulki na ɓangaren gwamnatin Ganduje na rubuta rahoton ƙarshe kafin miƙa mulki. Ya bayyana cewa kamata ya yi kwamitin karɓa na gwamnati mai jiran gado shi ma ya shirya domin karɓar rahoton, wanda ya yi alƙawarin miƙawa a kan lokaci.

Muhammad Garba ya ƙara da cewa manufar miƙa mulki shi ne gwamnati mai sauka ta miƙa duk wasu abubuwa na tafiyar da shugabanci cikin ruwan sanyi. Ba yunkurin yaɗa wani tunani ko wata aƙida ba.

Ya kuma ce kamata ya yi gwamnati mai jiran gado ta mayar da hankali game da shirin da take yi na karɓar mulki, ta kuma kiyaye duk wani abu da zai iya janyo fitina a yayin miƙawar.

Ƙorafin da NNPP ta yi a jiya shi ne gwamnatin ta ba ta gurbi uku kawai a cikin kwamitin da aka kafa don miƙa mulki hannun sabuwar gwamnati.

BBC 

Saturday, 28 January 2023

Bayan Zargin Yi Wa Takararsa Zagon Kasa, Tinubu Ya Ziyarci Buhari A Daura

 


Yan kwanaki bayan ya zargi Gwamnatin Tarayya da kokarin yi wa takararsa kafar ungulu, ta hanyar wasu manufofinta, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a mahaifarsa da ke Daura a Jihar Katsina.

Tinubu dai ya sami rakiyar Gwamnan Jihar ta Katsina, Aminu Bello Masari da wasu Gwamnonin APC, yayin ziyarar da daren Juma’a, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar wa Aminiya.

Sai dai babu cikakkun bayanai kan ainihin makasudin ziyarar ta Tinubu zuwa Daura.

A ranar Alhamis ce Aminiya ta rawaito yadda Tinubu ya yi zargin gwamnati mai ci ta kirkiro matsalar wahalar man fetur da canjin kudin da suka jefa ’yan Najeriya cikin kunci a ’yan kwanakin nan da gangan ne domin ta gurgunta takararsa.

Lamarin dai ya yi ta yamutsa hazo a fagen siyasar Najeriya, inda wasu suke zargin akwai alamun baraka tsakanin dan takarar da gwamnatin jam’iyyarsa.

Amma Kakakin Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, Byo Onanuga, ya zargi ’yan adawa da kokarin rura wutar, inda ya ce suna kokarin haddasa fitina ne kawai ta hanyar juya masa magana.

Kazalika, ita ma Fadar Shugaban Kasa ta ki ta ce uffan a kan batun, kodayake akwai rade-radin cewa ziyarar ta Tinubu na da alaka da kalaman nasa


A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, “Tinubu ya gana da Gwamna Aminu Bello Masari na Katsina da Babagana Umara Zulum na Borno da kuma na Kebbi, Atiku Bagudu, kafin su rankaya su tafi Daura wajen Buhari, kodayake Zulum bai bi su ba.

“Watakila Tinubun ya fuskanci duk inda suka je kamfe suna fuskantar matsala daga mutane, shi ya sa ya ga ya dace ya tattauna da Shugaban a kan lamarin,” in ji majiyar.

AMINIYA

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...