Posts

Showing posts with the label Cibiya

Cibiyar Koyar Da Ayyukan Hajji Ta NAHCON, Za Ta Fara Gudanar Da Harkokin Koyarwa

Image
Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Cibiyar Aikin Hajji  za ta fara gudanar da harkokin karatun ta na shekarar 2023/24 a ranar Talata 7 ga Fabrairu, 2023 rukunin farko na dalibai. Taron budewar wanda  Ministan ilimi, Adamu Adamu zai kaddamar da da shi, yayin da ministan babban birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, zai kasance babban bako na musamman. A sanarwar da mataimakin daraktan harkokin yada labarai da hulda da jama’a na hukumar NAHCON, Mousa Ubandawaki, and yace Cibiyar za ta fara ne da shirin sati 4 na bayar da takardar shaida ga dalibanta na "Tsarin Gudanar da Ayyukan Hajji da Umrah". Shugaban hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, ya bayyana farin cikinsa da kafuwar wannan cibiya. “Muna gaggauta taya dukkan masu ruwa da tsakinmu murnar wannan nasarar da muka samu. Ba za mu iya yin da'awar cewa mun cimma wannan kawai ba. Don haka, mun fahimci gudummawar da hukumar da ta gabata ta bayar. Don haka ina kira ga masu ruwa da tsaki da su hada kai a matsay...