Akwai Yiwuwar Matsalar Tsaro Ta Kawo Wa Zaben 2023 Tangarda – INEC

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi gargadin cewa matsalar tsaron da ake fama da ita a wasu sassan Najeriya za ta iya sa wa a soke babban zaben 2023 da za a fara a watan gobe. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu, wanda Shugaban Cibiyar Bincike Kan Harkokin Zabe (BEI), Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ya wakilta ne ya yi gargadin ranar Litinin a Abuja. Ya bayyana hakan ne yayin wani taron ba da horo kan shirye-shiryen tsaro a lokacin zaben. Hukumar ta ce matsalar na iya sa wa a gaza gudanar da zaben a mazabu da dama, ta yadda zai yi wahala a iya bayyana wanda ya lashe shi, wanda ta ce hakan zai haifar da rudani a tsarin mulkin Najeriya.