Search This Blog

Showing posts with label Zabe. Show all posts
Showing posts with label Zabe. Show all posts

Wednesday, 31 July 2024

Labari Da Dumiduminsa: Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kano Ta Sanar Da Ranar Zaben Kananan Hukumomi

Shugaban Hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, shi ne ya sanar da hakan a safiyar ranar Laraba, yayin da yake yi wa manema labarai bayani 

Malumfashi ya kara da cewa Hukumar za ta gudanar da zaben ne a ranar 30 ga Watan Nuwanba na 2024

Yayi amfani da taron wajen yin Kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki, su tallafawa Hukumar don gudanar da sahihin zabe

Cikakken Labarin zai zo muku nan gaba 

Saturday, 3 February 2024

INEC Ta Dakatar Da Sake Zabe A Enugu, Kano, Akwa Ibom Sakamakon Rikici, Sace Jami'an Zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da sake gudanar da zabukan da aka gudanar a wasu mazabu na jihohin Enugu, Kano, da Akwa Ibom, sakamakon tarzoma, da rashin bin ka’ida, da kuma sace jami’an zabe.

Yankunan da abin ya shafa sun hada da mazabar Enugu ta Kudu 1 a jihar Enugu, da kuma mazabar tarayya ta Ikono/Ini a jihar Akwa Ibom, da kuma mazabar Kunchi/Tsanyawa dake jihar Kano.

Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sam Olumekun, kwamishinan na kasa & shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, a ranar Asabar.

Dakatarwar ta biyo bayan rahotannin ‘yan daba da sace kayan zabe a wadannan jihohin. A mazabar Enugu ta Kudu 1, an dakatar da zabukan a dukkan runfunan zabe takwas da aka yi na farko

A mazabar Kunchi da Tsanyawa da ke jihar Kano, an dakatar da zabuka a dukkanin mazabu goma da ke karamar hukumar Kunchi sakamakon mamayewa da barna da kuma kawo cikas da ‘yan daba.

An yanke wannan hukuncin ne bisa ga sashe na 24(3) na dokar zabe ta 2022. INEC ta bayyana cewa za ta sanar da karin matakan da za ta dauka kan mazabar da abin ya shafa bayan wani taro a ranar Litinin da ta gabata, sannan ta gayyaci jami’an tsaro da su binciki lamarin. Hukumar ta kuma yi alkawarin yin nazari sosai kan duk wani sabani da ya shafi jami’anta.


Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na gudanar da zabuka a kananan hukumomi 80 da ke fadin jihohi 26 domin cike gurbi a kananan hukumomi 3, da na tarayya 17 da kuma mazabu na jiha 28 da suka yi rajista 4,904,627, wadanda 4,613,291 suka karbi katin zabe na dindindin (PVCs).

(Leadership Newspaper)

Tuesday, 18 April 2023

Yau INEC Za Ta Taron Gaggawa Kan Zaben Adamawa

A yau Talata Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta gudanar ta taron gaggawa da ta kira kan dambarwar sakamakon zaben gwamnan Jihar Adamawa da ya tayar da kura.

Daga taron ne za a ji shawarar da INEC ta yanke a game da sakamakon zaben gwamnan, wanda a ranar Lahadi hukumar ta dakatar da tattarawa saboda rikicin da ya dabaibaye shi.


A ranar Litinin hukumar ta dakatar da Kwamishinan Zabe (REC) na Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunus Ari, saboda ya yi gaban kansa wajen ayyana Sanata Aisha Dahiru Binani ta Jam’iyyar APC a matsayin zababbiyar gwamna, alhali ba a kammala tattara sakamakon zaben ba.

Lamarin dai ya yamutsa hazo, amma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, wanda yake neman a zaben a Jam’iyyar PDP, ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, domin INEC za ta dauki matakin da ya dace.


Tuni dai Fintiri da PDP da kungiyoyin kare dimokuradiyya suka yi tir da abin da kwamishinan zaben ya yi, inda suka bukaci INEC ta dauki mataki a kan wannan kwamacala.

Rikicin zaben ya dauki sabon salo ne a safiyar Lahadi a yayin da ake tsaka da jiran lokacin da za a karbi sakamakon kananan hukumomi 10 bayan an karasa zaben a ranar Asabar, amma Barista Hudu ya yi riga-malam-masallacin sanar da cewa Binani ta yi nasara.

Amma daga bisani Hedikwatar INEC ta soke ayyanawar da da Hudu ya yi, cewa haramtacce ne, ba shi da tasiri, sannan ba huruminsa ba ne sanar da sakamakon zabe, aikin Jami’in Tattara Sakamakon Zaben, Farfesa Mele Mohammed ne.


Daga nan Hukumar ta ba da umarnin dakatar da tattara sakamakon zaben, sannan ta umarci Hudu da Farfesa Mohammed da wakilan jam’iyyun da suka shiga zaben da sauran masu ruwa da tsaki su bayyana da hedikwatarta da ke Abuja domin lalubo bakin zaren.


An gudanar da karashen zaben ne a ranar 15 ga watan Afrilu, bayan da INEC ta ayyana wanda aka fara gudanarwa a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammalu ba, saboda soke kuri’un wasu rumufanan zabe da aka yi sakamakon aringizon kuri’u da rigingimun da aka samu a lokacin zaben na farko.
AMINIYA 

Thursday, 16 March 2023

Za Mu Kama Duk Wanda Ya Dauki Makami Ranar Zabe A Kano —’Yan Sanda

 


Mataimakin babban sufeto-Janar na ’yan sanda DIG Hafiz Muhammad Inuwa da ke kula da harkokin zaben shekarar 2023 a yankin jahohin Arewa maso Yammacin Najeriya, ya gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu, da su kauce wa yin wani abu da zai tada hankulan masu zabe. 

DIG Hafiz M. Inuwa ya bayyana cewa shugaban ’yan sanda Usman Alkali Baba ya umarce su, da su gargadi ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki da su ja wa magoya bayansu kunne gabanin zaben da ke tafe a ranar Asabar 18 ga watan Maris 2023.

Ya bayyana hakan ne a Jihar Kano, a ci gaba da shirye-shirye da rundunar ke yi na tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu.

Ya kara da cewa fatansu, shi ne a yi zabe lafiya a kammala lafiya, ba tare da nuna siyasa da gaba ba.“Duk wani dan siyasa in dai yana son ci gaban Kano, to zaman lafiya shi ne ci gaban, so ake a zauna lafiya.

“Kuma na zo da jawabi, in gargade su, Wallahi ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen maganin duk wani da ya nemi ya tada fitina,

“Saboda haka ina tabbatar muku da cewa duk wanda ya nemi ya dau makami ko don ya hana wani fitowa zabe, ko don ya jikkata wani, to Wallahi Tallahi fushin hukuma ne a tattare da shi” in ji shi.Ya ce ba zu raga wa kowa ba duk girmansa kowaye , domin ci gaban Nijeriya da ci gaban Kano da kuma zaman lafiya shi ne agaban mu.

Tun kafin wannan lokacin ne Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa sun tanadi ’yan sanda masu yawa don tabbatar da tsaro a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.

Tuesday, 21 February 2023

INEC Ta Gargadi Masu Sanya Idanu Kan Zaben Najeriya

Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC, ta gargaɗi masu aikin sa ido kan yadda zaɓukan ƙasar za su gudana su kiyaye da dokoki da ƙa'idojin ƙasar sannan su guji katsa-landan a abin da ba su da hurumi a kai.

INEC ta yi gargaɗin ne a lokacin da ta gudanar da taron ƙarin haske game da dokokin aikin sa idon da bayar da bayanai ga masu aikin na cikin gida da kuma na waje a Abuja, ranar Talatar nan.

Tuni dubban masu sa idon suka hallara a ƙasar domin duba yadda zaɓukan - da za a fara ranar Asabar 25 ga watan nan na Fabarairu - za su gudana, inda za a fara da na shugaban ƙasa da na 'yan majalisun dokoki na tarayya.

Sai kuma ranar 11 ga watan Maris inda za a yi zaɓukan gwamnoni da 'yan majalisun dokoki na jihohi

Dubban masu sanya idanu daga ƙungoyoyi daban-daban na ciki da wajen Najeriya ne suka saurari bayanai daga manyan jami'ai na hukumar zaɓen da suka haɗa da shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu da sauran muƙarraban hukumar game da yadda kowa zai taka rawar da ta dace ba tare da wuce gona da iri ba a kan zaɓukan.

Farfesa Sani Adam wanda kwamishina ne a hukumar zaɓen ta Najeriya ya yi wa BBC ƙarin bayani a kan gargaɗin da suka yi wa masu aikin sa idon, inda ya ce suna so jami'an su kasance mutane masu adalci ba kuma 'yan leƙen asiri ƙasa ba.

Farfesan ya ce suna son su kasance sun dubi abin da ake yi kuma su tabbatar duk ƙa'idojin da aka gindaya musu sun kiyaye da su, sannan a bi zaɓen kamar yadda ake ba tare da an samu tashin hankali ba

Kwamishinan ya ce suna so masu sa idon, su kasance sun bayar da bayani kan abubuwan da suka gani na gaskiya sannan su kasance masu bin dokokin Najeriya da kuma zaɓen.

Bayan wannan kuma kar su yi katsa-landan a ciki, kar su shiga harkar da ba ta shafe su ba.

Jami'in ya ce, ''masu aikin suna da damar bayar da bayanin duk abin da suka gani su tabbatar haka ne.''

Ya ce, ''akwai dokoki waɗanda suka ba masu aikin sa idon, '' mun ƙarfafa gaya masu cewa Najeriya ƙasa ce mai zaman kanta ba ƙasa ba ce da za su zo su yi mata katsa-landan,'' in ji shi.

''Amma su yi aikinsu yadda ake so kuma su yi aiki ne don su taimaka mana wajen ƙara gyara yadda ake zaɓe a Najeriya,'' a cewarsa.

Shi kuwa Salisu Musa mai sa ido daga ƙungiyar 'Country International Human Right Movement', ya gaya wa BBC cewa a matsayinsu na masu sa ido na waje ''dole mu ɗauki ƙa'idojin da suka bayar.

''Amma akwai abubuwan da INEC suka faɗa kusan za mu saurare su mu ji'', in shi ji.

''Amma za mu saka ido duk abin da muka ga ya yi ba daidai ba za mu sa shi a cikin rahoto don kowa ya same shi,'' in ji shi.

Musa ya ce, ''ka san daman kusan ita wannan observers kamar ba ta shiri da INEC saboda abin da ake gani sun zo don su bi ƙwaƙwaf kan me ke faruwa,''

''Ka san ba za ka so ya zamanto ya yi maka babakere a gida ba,'' in ji mai sa idon.

''Ita maganar wannan katsa-landan suna nufin dole mu bi a hankali tun da dukkanmu ƙungiyar da ta zo wajen aikin nan dole muna da tsare-tsarenmu, kuma za mu tabbatar namu bai ƙetare na hukumar zaɓen ba,'' in ji shi.

Shugaban hukumar zaɓen ta Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce wannan zaɓe shi ne wanda ya fi samun masu sa ido na ciki da na waje a tarihin zaɓen Najeriya.
BBC 

Friday, 13 January 2023

Sabbin Katinan Zabe 13m Muka Buga —INEC


Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na bincike kan zargin jami’anta da karbar na goro a aikin rabon katin zabe da ke gudana.

Hukumar ta kara da cewa ta buga sabbin katinan zabe miliyan 13 da dubu 868 da 441 bayan kammala aikin rajistar sabbin masu zabe.

Da yake sanar da hakan, Kwamishinan INEC na Kasa kan Wayar da Masu Zabe da Yada Labarai, Festus Okoye, ya ce, “Hukumar ta damu bayan samun korafe-korafe kan nuna fifiko a wasu wuraren rabon katin.

“Duk halastattun masu rajista na da ’yancin karbar katinsu domin kada kuri’a a ranar zabe a wuraren da suka yi rajista.”

“Domin kawar da shakku, sabbin katunan zabe miliyan 3 da dubu 868 da 441 INEC ta buga da suka hada da na sabbin wadanda suka yi rajista da wadanda suka sauya wurin zabe da kuma wadanda aka sabunta katinsu.”

Okoye ya sanar cewa hukumar ta kara lokacin rabon katin zuwa ranar 29 ga watan Janairu da muke ciki, daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana, har da ranakun Asabar da Lahadi.

Hukumar ta kuma umarci jami’anta masu aikin rabon katin da su tattara duk wani korafi rashin buga kati zuwa ga shugabanninsu a jihohi domin daukar matakin da ya dace.

(AMINIYA)

Thursday, 12 January 2023

Kamawa zasu maimaita abun da ya faru a zaben 1993 - Ganduje

Abdullahi Umar Ganduje, ya ce Kanawa za su sake maimaita abin da ya faru a zaben Shugaban Kasa na 1993, inda suka goyi bayan dan takarar da ya fito daga yankin Kudu – suka yi watsi da nasu na Arewa kuma dan asalin jihar.

Ganduje ya yi wannan furuci ne a yayin wani rangadin yakin neman zabe da ya fita tare da ’yan takarar jam’iyyar APC masu neman mukamai daban-daban a zabe mai zuwa.


Aminiya ta ruwaito cewa gwamnan ya yi furucin ne yayin da ya ziyarci Hakimin Kibiya, Sunusi Abubakar Ila, bayan gudanar da taron yakin neman zabe da tuntubar juna a kananan hukumomin Rano da Bunkure na jihar.

A zahiri dai Ganduje ya tabbatar da goyon bayansa ga dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, inda ya yi hannun riga da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ke takarar kujerar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP.

A jawabinsa yayin hikaito tarihi, Ganduje ya ce, “Mun zabi Cif MKO Abiola na jam’iyyar SDP kuma muka ki amincewa da Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC saboda dukkanmu mun yi imani da hadin kan kasa da la’akari da cancanta.

“Sanin mu ne cewa Tinubu ya kasance ginshiki wajen fitowar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar Action Congress (AC).

“Ya [Tinubu] kuma tsaya tsayin daka wajen ganin Nuhu Ribadu ya zama dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).

“Saboda haka, Asiwaju Tinubu ya yi aiki tukuru wajen ganin an samu daidaito, kuma a baya ya rika fadi–tashi wajen goyon bayan ’yan takarar Shugaban Kasa da suka fito daga a Arewa.

“Duba da wannan dalili, ya cancanci mu saka masa da irin alherin da ya yi. Kuma a yanzu ba mu da wani zabi da ya wuce mu goyi bayan takararsa.

“A halin yanzu Tinubu shi ne daya tilo wanda ya cancanta kuma ya fi cancantar takarar Shugaban Kasa a zabe mai zuwa.

“Ba zai gushe ba Arewa na goyon bayansa saboda akidarsa ta gina kasa, da sanin ya kamata, da tsayuwar daka ga ci gaban bil’adama da kasa, da dai sauran abubuwa,” in ji Ganduje.

Monday, 9 January 2023

Akwai Yiwuwar Matsalar Tsaro Ta Kawo Wa Zaben 2023 Tangarda – INEC



Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi gargadin cewa matsalar tsaron da ake fama da ita a wasu sassan Najeriya za ta iya sa wa a soke babban zaben 2023 da za a fara a watan gobe.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu, wanda Shugaban Cibiyar Bincike Kan



Harkokin Zabe (BEI), Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ya wakilta ne ya yi gargadin ranar Litinin a Abuja.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron ba da horo kan shirye-shiryen tsaro a lokacin zaben.

Hukumar ta ce matsalar na iya sa wa a gaza gudanar da zaben a mazabu da dama, ta yadda zai yi wahala a iya bayyana wanda ya lashe shi, wanda ta ce hakan zai haifar da rudani a tsarin mulkin Najeriya.

Wednesday, 4 January 2023

Mutanen Kano sun tabbatar min da yakinin zan lashe zabe - Tinubu



Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewar yana da yakinin jam’iyyar za ta kai ga nasara duba da irin fitowar dangon-kwari da magoya suka yi mata a Jihar Kano.

Jaridar Aminiya ta rawaito cewa A ranar Talata ce dai Tinubu ya ziyarci Kano don kaddamar da yakin neman zabensa a Arewa Maso Yamma, gabanin shiga zaben Shugaban Kasa a wata mai kamawa.

Da yake jawabi ranar Laraba a filin wasa na Sani Abacha, Tinubu ya ce, “Manuniya ta nuna cewa a yakin neman zaben nan, jama’ar Kano sun san abin da ya kamata su zaba.

“Ina da yakinin goyon bayan da Gawuna da Garo ke samu zai kai jam’iyyar nan ga nasarar lashe zaben gwamna har zuwa na Shugaban Kasa,” in ji Tinubu.

Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda mutane suka yi dafifi don nuna goyon bayansu ga takararsa.

A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci magoya baya da su kada wa jam’iyyar APC kuri’arsu a babban zaben da ke tafe.

Ganduje ya bai wa Tinubu tabbacin cewar kuri’ar jama’ar Kano ta APC ce duba da yadda mutane ke mararin sake ganin jam’iyyar ta mulke su.

Haka kuma, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bukaci jama’ar yankin Arewa maso Yamma da su sake zabar APC don dorawa daga inda Shugaba Muhammadu Buhari zai tsaya.

Adamu, ya ce irin jama’ar da suka tarbi Tinubu a Kano, wata ‘yar manuniya ce da ke nuna alamar jam’iyyar za ta kai ga nasara.

Shugaban APC na kasa, ya mika tutar jam’iyyar ga dan takarar Gwamnan Jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda shi ne Mataimakin Gwamnan Jihar a yanzu.

Daga cikin wadanda suka halarci taron yakin neman zaben a Kano; akwai Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu da Shettina, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato tare da gwamnonin Jihohin Arewa Maso Yamma da suka hada da Jigawa, Katsina, Zamfara, Kebbi da kuma Kaduna

Monday, 2 January 2023

Obasanjo ba zai iya kawo mazabarsa ba - Tinubu


Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya gargadi Peter Obi, cewa kada ya rudu da goyon bayansa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ke yi.

Tinubu ya ce goyon bayan Obasanjo ba zai kai Peter Obi ko’ina ba, saboda Obasanjo ba zai iya lashe akwatin mazabarsa ba.

“Bincikenmu mun gano Obasanjo bai taba nasarar sa wani ya lashe kujerar shugaban kasar Najeriya ba.

“Ko a Jihar Ogun babu wanda zai dogara da shi don lashe kujerar gwamna ko kansila,” in ji Tinubu  ta hnnun Daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben Tibubu, Bayo Onanuga.

Ya ci gaba da cewa, “Muna tausaya wa Peter Obi domin Obasanjo ba zai iya lashe masa akwatin mazabarsa da ke Abeokuta ba a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.”

Tsohon gwamnan na Legas, ya bayyana yadda Obasanjo ya goyi bayan tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar a zaben 2019 kuma ya sha kaye a hannun Shugaba Buhari.

Tinubu ya jadadda cewa da taimakonsa Buhari ya samu gagarumar nasara a zaben tare da tika Atiku da kasa.

Ya ce tarihi ne zai sake maimaita kan sa a zaben da ke kara kartowa a watan Fabrairu.


Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...