Gwamnatin Tinubu Ce Za Gudanar Da Kidaya —Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a dage lokacin gudanar da Kidayar Jama’a da Gidaje da aka shirya farawa ranar 3 ga watan Mayu mai kamawa. Kwana hudu kafin fara aikin Buhari ya ce ya bai wa gwamnati mai jiran gado damar yanke shawara kan lokacin gudanar da kidayar domin tabbatar da nasararsa. Ya sake dage lokacin gudanar da kidayar ne bayan wata ganawa da tsakanin Shugaba Buhari da shugaban hukumar, Nasir Isa Kwarra tare da Majalisar Zartarwa ta Tarayya a ranar Juma’a a Fadar Shugaban Kasa. Sanarwar da Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed ya fitar ta ce duk da haka Shugaba Buhari ya jaddada muhimmancin gudanar da kidayar wadda rabon da a gudanar shekara 17 ke nan. Shugaban ya kuma yaba da kyakkyawatan shirin da hukumar ta yi wa kidayar, wanda zai tabbatar da ingancinsa kamar na sauran kasashen duniya. Wata majiya a hukumar ta ce an dage aikin kidayar ne saboda wasu matsalolin da hukumar ke fuskanta da za su hana ta gudanar da aikin a lokaci guda; sai dai ba ta yi kari