Sababbin Shugabannin NAHCON Sun Kama Aikinsu Bayan Da Mataimakin Shugaban Kasa Ya Kaddamar Da Su
A ranar Laraba ne Hukumar kula da aikin Haji ta kasa ta shaida wani muhimmin lamari, yayin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kaddamar da shugabancinta a karo na biyar karkashin jagorancin Malam Jalal Ahmed Arabi Taron kaddamarwar ya faru ne a ofishin mataimakin shugaban kasar, inda bayan nan ne shugabannin suka zarce zuwa hukumar A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace a yayin gudanar da taro shugabannin hukumar ta NAHCON, shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi, yayi maraba da dukkanin wakilaninda ya bayyana kwarin gwiwarsa ga cancantarsu, inda ya kuma basu tabbacin samun hakan daga bangaren ma'aikatan hukumar kamar yadda shi ma ya samu yayin da ya kama aiki a watanni hudun da suka gabata. Daga nan sai yayi kira ga ma'aikatan hukumar su bayar da makamancin hadin kan sababbin shugabannin nasu don cimma manufar hukumar Sababbin shugabannin da aka nada sun ...