Posts

Showing posts with the label Edo

Jami'an tsaro sun kuɓutar da fasinjojin jirgin ƙasan Edo 12

Image
Hukumomin jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ce an kuɓutar da fasinjoji 12 na jirgin ƙasa, da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a tashar jiragen ƙasa da ke jihar a makon da ya gabata. An kama wasu daga cikin 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su, to sai dai wasu daga cikinsu sun tsere tare da wasu fasinjojin biyu a lokacin da jami'an tsaro ke ƙoƙarin kuɓutar da su. Hukumomin jihar sun ce an kuɓutar da mutanen 12 a lokacin da jami'an tsaro suka yi wa masu garkuwa da mutanen kwanton ɓauta. Tuni aka kai mutanen da aka kuɓutar ɗin asibiti domin duba lafiyarsu. Gwamnatin jihar ta alƙawarta ci gaba da nemo sauran fasinjojin biyu da ke hannun 'yan bindigar. Gwamnan jihar ya soki hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta ƙasar kan gaza samar da tsaro kan tasoshin jiragen ƙasan duk da faruwar makamancin wannan hari a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar a shekarar da ta gabata. Tun da farko dai hukumomin sun ce mutum 32 ne 'yan bindigar suka yi garku...

Maharan Jirgin Edo Na Neman Fansar N520m

Image
’ Yan bindigar da suka sace fasinjoji a Tashar Jirgin kasa ta Ekehen da ke Jihar Edo na neman Naira miliyan 520 a matsayin kudin fansa. Rahotanni sun ce maharan sun kira iyalan fasinjoji 26 da ke hannunsu, suka yanka musu fansar Naira miliyan 20 a kan duk mutum daya. Zan dora daga inda El-Rufai ya tsaya a Kaduna —Uba Sani Kano 2023: Dalilin ba wa Gawuna takarar Gwamna —Ganduje Wani shugaban matasa a yankin, Benson Ordia, da ya tabbatar da hakan, ya ce gwamnatin jihar ta ce za ta gudanar da bincike na tsanaki a yankin. Sai dai kakakin ’yan sandan jihar, Chidi Nwanbuzor, ya ce ba shi da masaniya kan kudin fansar da maharan suka yanke kan fasinjojin. A ranar Asabar ce maharan suka kai hari tare da yin awon gaba da fasinjoji akalla 32 a tashar jirgin kasan. Sai dai jami’an tsaro sun ceto mutum shida daga cikin fasinjojin jirgin kasan da aka sace, wadanda uku daga cikinsu kananan yara ne. Wannan dai shi ne karo na biyu da ’yan bindiga ke kai wa jirgin kasa hari tare da sace fasi...

Gwamnatin Najeriya ta rufe tashar jirgin ƙasa a Edo bayan harin 'yan bindiga

Image
  Copyright: O Hukumomi a Najeriya sun sanar da rufe tashar jirgin ƙasa ta Ekehen da ke jihar Edo, sa'o'i kaɗan bayan hari da 'yan bindiga suka kai tare da yin awon gaba da fasinjojin da ba a san adadinsu ba. Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da fasinjojin ke shirin hawa jirgin ƙasan zuwa garin Warri da ke jihar Delta Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzor, ya ce kawo yanzu ba su samu labarin rasa rai ba. To sai dai ya tabbatar da cewa wasu fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga daga maharan. Ya ce 'yan bindigar ɗauke da bindigogi sun far wa tashar jirgin ƙasan da maraicen ranar Asabar, inda suka riƙa harbi a sama kafin su kama wasu da yawa daga cikin fasinjojin. Lamarin na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan da 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a arewacin ƙasar tare da yin garkuwa da fasinjoji ma...