Gwamnatin tarayya za ta dena biyan tallafin man Fetur
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce daga ƙarshen watan Yunin wannan shekara za ta daina biyan tallafin man fetur a ƙasar.
Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta ƙasar Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a lokacin gabatar da kasasfin kuɗin shekarar 2023.
BBC Hausa ta rawaito cewa Misis Zainab ta ce gwamnatin tarayya ta ware kimanin naira tiriliyan 3.36 domin biyan tallafin man fetur ɗin a cikin wata shida na farkon shekarar 2023.
Ministar ta ƙara da cewa hakan na daga cikin tsarin tsawaita cire tallafin zuwa wata 18 da gwamnatin ta bayyana a shekarar da ta gabata.