Posts

Showing posts with the label Obasanjo

Malamai Da Tsofaffin Soji Ba Sa Kwazo A Jagoranci —Obasanjo

Image
Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce galibi ba a samun wani ci gaba na a zo a gani a jihohin da suka kasance karkashin jagorancin malamai ko tsofaffin soji. Obasanjo ya ce babu wani ci gaban da aka samu a jihohin kasar nan da ke karkashin jagorancin mutane masu rike da matsayin Farfesa ko Dakta da tsoffin sojoji, har ma da malaman makarantu. Tsohon Shugaban na Najeriya na wannan furuci a jawabinsa yayin wani taro kan zurfafa al’adun dimokuradiyya da aka gudanar ranar Alhamis a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Obasanjo ya ce duk da yake an samu wasu jajirtattun shugabannin da ba su da yawa, akasarinsu ba sa iya mulki mai kyau saboda rashin samun mataimaka na gari, abin da ke hana su jagorancin da ake bukata. A cewarsa, rashin tattaunawa tsakanin shugabannin da masu taimaka musu, kan haifar da gibi wajen musayar ra’ayi, matakin da ke hana samun fahimtar juna da hadin-kai wajen cimma manufar ci gaba da ake bukata. Obasanjo ya ce, bayan kwashe shekaru 60 da sa

Obasanjo ya zama tamkar dan bakin ciki - Fadar Shugaban kasa

Image
Fadar Shugaban Najeriya ta mayar da kakkausan martani kan kalaman da Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya fitar, sanarwar ta ce Obasanjo ba zai taɓa daina caccakar Shugaba Muhammadu Buhari ba sakamakon Obasanjon ba zai daina baƙin ciki kan duk wani wanda ya sha gabansa a ayyukan ci gaban ƙasa ba. Fadar shugaban ƙasar ta buga misali da cewa Shugaba Buhari ya kammala gadar Neja ta biyu bayan an yi shekara 30 ana alƙawura a kanta. Haka kuma fadar shugaban ƙasar ta ce Obasanjo ya yi wa kudu maso gabashin Najeriya ƙarya domin ya samu ƙuri'unsu, amma Shugaba Buhari bai samu ƙuri'unsu ba amma duk da haka sai da ya yi musu aikin gadar. Fadar shugaban ƙasar ta kuma ce Obasanjo yana baƙin ciki ne sakamakon yana ganin yadda Buhari ke samun lambobin yabo da kuma yadda shugaban ke ci gaba da da'awar cewa zai tabbatar an gudanar da sahihin zaɓe fiye da wanda

Obasanjo ba zai iya kawo mazabarsa ba - Tinubu

Image
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya gargadi Peter Obi, cewa kada ya rudu da goyon bayansa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ke yi. Tinubu ya ce goyon bayan Obasanjo ba zai kai Peter Obi ko’ina ba, saboda Obasanjo ba zai iya lashe akwatin mazabarsa ba. “Bincikenmu mun gano Obasanjo bai taba nasarar sa wani ya lashe kujerar shugaban kasar Najeriya ba. “Ko a Jihar Ogun babu wanda zai dogara da shi don lashe kujerar gwamna ko kansila,” in ji Tinubu  ta hnnun Daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben Tibubu, Bayo Onanuga. Ya ci gaba da cewa, “Muna tausaya wa Peter Obi domin Obasanjo ba zai iya lashe masa akwatin mazabarsa da ke Abeokuta ba a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.” Tsohon gwamnan na Legas, ya bayyana yadda Obasanjo ya goyi bayan tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar a zaben 2019 kuma ya sha kaye a hannun Shugaba Buhari. Tinubu ya jadadda cewa da taimakonsa Buhari ya samu gagarumar nasara a zaben tare da ti

2023: Peter Obi Ne Dan Takarata —Obansajo

Image
  A karon farko tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya fito bainar jama’a ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, a zaben 2023. Da yake bayyana goyo bayan nasa a cikin sakonsa na murnar shiga Sabuwar Shekarar 2023, Obasanjo ya ce Peter Obi ya yi wa sauran ’yan takarar shugaban kasa fintinkau wajen  ilimi da kwarewa. https://noordakata.blogspot.com/2023/01/abdulmumin-jibrin-kofa-ya-raba-tallafin.html https://noordakata.blogspot.com/2023/01/gwamnan-jihar-kano-abdullahi-umar.html A cikin sakonsa nasa mai mai taken, “Rokona ga ’yan Najeriya, musamman matasa,” Obasanjo ya ce, “Duk da cewa a cikin masu masu takarar babu wani shafaffe da mai, amma a cikin Peter Obi ya fi sauran nagarta ta bangaren kyawun dabi’u, gogewa, fahimta, abin da suka yi a baya da wanda za su iya kawowa.” “Sauran kuma, kamar kowannenmu na da irin gudunmawar da zai bayar a sabuwar gwamantin wajen farfado da al’amura da kuma ceto Najeriya. “Dadin dadawa, Peter Obi allura da