Search This Blog

Showing posts with label Dan ta'adda. Show all posts
Showing posts with label Dan ta'adda. Show all posts

Tuesday, 16 May 2023

Wani dan ta'adda ya tarwatsa kansa da bam a Kaduna

 


Jama'a sun shiga firgici a jihar Kaduna ta Najeriya bayan wani mutun da ake zargin dan ta'adda ne ya tarwatsa kansa da bam a daidai lokacin da jami'an tsaro ke kokarin cafke shi, yayin da gawarsa ta yi kaca-kaca.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Ibrahim Haske da ke unguwar Keke a Millenium City a sanyin Safiyar wannan Litinin. 

Mutanen da lamarin ya auku a kan idanunsu sun ce, an yi jin karar harbe-harben bindiga da misalin karfe 1 na cikin daren da ya gabata lokacin da jami'an tsaron farin kaya na DSS da sojoji suka dirar wa gidan dan ta'addar da ake zargi.

Mutumin ya tarwatsa kansa ne da bam din bayan ya fahimci cewa, jami'an tsaron sun yi masa zobe.

Rahotanni sun ce, mutumin ya dauki lokaci yana musayar wuta tsakaninsa da jami'an tsaro kafin yanke shawarar kashe kansa da kansa, yayin da aka gano bindiga kirar AK-47 a cikin gidansa da kuma wasu bama-bamai.

PUBLICITÉ

Tuni jami'an tsaro suka tafi da matar mutumin da 'ya'yansa bayan ya kashe kansa.

RFI

.

 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...