Posts

Showing posts with the label NDLEA

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi na kusan naira biliyan biyar

Image
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeroiya NDLEA ta ce ta kama wasu miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya kai naira biliyan biyar a wani gidan ajiye kayyaki. A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce ta gano tan bakwai na tabar wiwi a jihohin Legas da Borno da Edo da Enugu da Katsina da kuma birnin tarayya Abuja. Hukumar ta ce daga cikin miyagun ƙwayoyin da ta gano sun haɗar da ƙwayar tramadol da yawanta ya kai 3,264,630, da kwalaben kodin 3,490 da wasu ƙwayoyin. Yayin da yake yaba wa jami'an na NDLEA bisa wannan namijin ƙoƙari, shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya yi kira a gare su da su ƙara tsage dantse domin kawo raguwar ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

Mun Kama Bako Da Kullin Hodar Iblis 105 Daga Brazil —NDLEA

Image
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama kullin hodar iblis 105 a cikin kayan wani wanda ya dawo daga kasar Brazil a Babban Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Legas. Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya sanar ranar Lahadi a Abuja cewa sun kama wanda ake zargin ne ranar Kirsimeti. Ya ce wanda ake zargin na daga cikin fasinjojin da suka dawo daga birnin Sao Paulo na kasar Brazil. A cewarsa, bayanan sirrin da suka samu sun taimaka wajen kama wanda ake zargin a filin jirgin. Ya ce, saura kiris ya sha sakamakon babu abin da suka gano a binciken farkon da suka yi masa. Da aka tsananta bincike a kansa karo na biyu, sai aka gano hodar iblis din da yake dauke da ita, in ji jami’in. Shugaban NDLEA na Kasa, Birgediya-Janar Buba Marwa (Murabus), ya sha nanata cewa ba za su raga wa masu fataucin miyagun kwayoyi ba ko’ina suke a fadin kasa. (AMINIYA) (NAN)