Posts

Showing posts with the label Kasar Saudiyya

Rahoton Aikin Hajji: Saudia Ta Cancanci Yabo Ba Kushe Ba .

Image
Kungiyar daukar rahotannin Hajji mai zaman kanta (IHR) na sane da kalubalen da aka fuskanta a aikin Hajjin bana sakamakon sauya manufofin da hukumomin Saudiyya suka yi a baya-bayan nan game da hidimar alhazai. Wadannan kalubalen sun taso da batutuwa da dama daga kasashen da suka halarci aikin Hajji wadanda kafafen yada labarai suka yi ta yadawa. Kungiyar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetan ta na kasa, Ibrahim Muhammed ta ce “Abu ne mai kyau cewa alhazai sun cancanci a yi musu hidima daidai da ayyukan da ake biya. "Duk da haka, yin hidima ga mahajjata sama da miliyan 2.3 ta hanyar samar da masauki, sufuri, ciyarwa, Aikin kula da lafiya da jagora a wuri guda, a lokaci guda yana buÆ™atar tallafin sassa da yawa da haÉ—in gwiwar duk wanda abin ya shafa," in ji sanarwar. Sanarwar ta kuma ce, galibin kasashen da ke halartar aikin Hajji sun dora alhakin ayyukan  da aka yi a wannan shekara musamman a tsawon kwanaki biyar a Mashaer. “Duk da cewa mun amince d...