Posts

Showing posts with the label kungiyar dalibai

Muna buƙatar Buhari ya sa baki kan ƙarin kuɗin makaranta - Kungiyar Dalibai

Image
Ƙungiyar Ɗalibai ta Najeriya NANS ta buƙaci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya yi ''gaggawar sa baki'' game da ƙarin kuɗin makaranta da jami'o'in ƙasar ke shirin yi tun kafin hakan ya janyo matsaloli a faɗin ƙasar''. Sakataren ƙungiyar na ƙasa Usman Baba Kankia, ya shaida wa BBC cewa ''duk makarantun gwamnatin tarayya sun ƙaƙƙara kuɗaɗe fiye da kashi 250 cikin dari'', A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu daga cikin jami'o'in ƙasar suka bayyana ƙarin kuɗin makaranta. To sai dai Sakataren ƙungiyar ya ce suna zargin cewa makarantun sun samu umarnin ƙara kuɗin makarantar ne daga sama. Dalilin ya da sa kenan suka rubuta wasika ga shugaba ƙasa, inda suka buƙace shi a matsayinsa na uba, ya sa baki domin mayar da kuɗin makarantar yadda yake a baya. Wasu jami'o'in dai sun bayyana cewa sun yi ƙarin kuɗin makarantar ne domin samun damar gudanar da makarantun nasu. dalibai othersCopyright: others To sai dai ƙu