Posts

Showing posts with the label Mai gyaran wutar lantarki

An Kama Mai Gyaran Wuta A Cikin Likitocin Bogi Masu Aiki A Asibitoci Fiye Da 100 A Kano

Image
Gwamnatin Jihar Kano ta cafke wani mai gyaran wutar lantarki a cikin jerin likitocin bogi masu aiki a fiye da asibitoci da wuraren karbar magani 100 a jihar. Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, a duk cikin likitocin na bogi, guda daya ne kacal ya mallaki kwalin sakandire kamar yadda bayanan kwamitin masu bincike suka nuna. Haka kuma, an samu wani mai gyaran wutar lantarki a cikin jerin likitocin na bogi da yake duba marasa lafiya a wani asibiti mai gado takwas. An gano wannan asibiti ne dai tare da karin wasu 129 yayin binciken kwamitin da Shugaban Karamar Hukumar Tudun Wada, Ahmad Tijjani Matata ya kaddamar. Jagoran Kwamitin, Abubakar Musa Karafe, ya ce binciken na zuwa ne bayan jerin korafe-korafe da suka rika samu daga al’umma kan yawaitar asibitocin kudi da wuraren sayen magani a yankin. Karafe ya ce daya daga cikin likitocin bogin ya tsiyaya wa wata mata jini mai dauke da kwayoyin cutar HIV a jikinta, duk da kuwa cutar zazzabin cizon sauro kadai ta yi korafin tana fama da it