Gwamnatin Najeriya Ta Kara Farashin Man Fetur
Gwamnatin Najeriya ta ƙara farashin man fetur a hukumance da kashi 8.8 inda a halin yanzu farashin ya koma naira 185 daga 170. Shugaban masu gidajen mai masu zaman kansu reshen Jihar Kano Bashir Danmallam ya tabbatar wa BBC da ƙarin inda ya ce sun samu umarni daga gwamnatin tarayya. Sai dai dama tun kafin gwamnatin Najeriya ta yi wannan ƙarin farashin tuni wasu gidajen mai a Najeriya suke sayar da man a farashin da ya fi na hukuma. Akwai masu sayarwa kan 190 har zuwa 350 a wasu jihohi da ke faɗin ƙasar. Kafin yin wannan ƙarin, akwai gidajen mai da dama a fadin Najeriya waɗanda ba su iya sayar da mai saboda ƙarancinsa. Ƙarin farashin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ministar kuɗi ta Najeriya Zainab Ahmed ta tabbatar da cewa akwai yiwuwar a soma cire tallafin man fetur daga watan Afrilu. Makomar tallafin man fetur a Najeriya bayan Yunin 2023 5 Janairu 2023 Amfani biyar game da samun man fetur a Arewacin Najeriya 23 Nuwamba 2022 Akwai yiwuwar cire tallafin man fetur a ƙasar ...