Shugaban Hukumar NAHCON Ya Karbi Rahoto Kan Masaukin Alhazai Tare Da Alkawarin Sake Inganta Ayyuka
Mai rikon mukamin Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Ahmed Arabi, OON, fwc, ya ce ba da fifiko tare da inganta jin dadin mahajjata da ayyukansu shi ne babban aikin da Hukumar za ta gudanar a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024. A sanarwar da Mataimakin daraktan yada yada labarai da dab'i na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar rahoton kwamitin duba sharuÉ—É—an masauki da ciyarwa yau a dakin taro na hukumar Ya ce samar da ingantacciyar hidima aiki ne mai matukar muhimmanci da hukumar za ta bi domin cika aikinta tare da dorewar amana da amincewar jama’a da kuma alhazai. A cewarsa, gabatar da rahoton da shawarwari a cikinsa “zai taimaka matuka wajen farfado da kwarin gwiwa da amincewar mutane da alhazai musamman a gare mu. “Ina so in gode muku bisa sadaukarwar da kuka yi. Wannan rahoto da shawarwarin ba shakka za su ba da gudummawa don haÉ“aka hanyoyin ci gaba da aiwatar da abu...