Ka da ka shekara goma da mata daya - Sheikh Daurawa
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce shawarci maza cewa ka da su kuskura su shekara 10 da mace daya matukar suna da burin kara aure. Sheikh Daurawa, ya bayyana haka ne a zantawarsa da gidan rediyon Freedom da ke Kano haka ne, inda ya ce idan namiji ya kai wannan shekarun da mace daya, lokaci ya kure masa. “Kada ka wuce shekara 10 idan za ka kara aure ba ka kara ba. Idan ka wuce shekara 10 akalla kana da ‘ya ‘yar shekara takwas ko tara. “Da zarar ’yarka ta kai shekara 15 ba ka kara aure ba, to wacce zaka auro da wuya ta wuce shekara 20. Za ka ga tsakaninsu da ’yarka bai wuce ’yan tazarar shekaru ba. “Saboda haka matarka ta samu abokiyar rigima. Akwai wadda za ta iya tura ’yarta ta samu amarya su rika rigima ko ta yi ta dukan amaryar saboda ta fi karfinta. “…Saboda haka wanda zai yi aure ya shirya da wuri, kuma kada duk dadin miyar mace ka ce ba za ka kara aure ba,” in ji Shehun malamin. Karin aure ko yi wa uwar gida kishiya na tayar da kura...