Search This Blog

Showing posts with label Kalandar Musulunci. Show all posts
Showing posts with label Kalandar Musulunci. Show all posts

Tuesday, 18 July 2023

1445 AH : Gwamnatin Kano Ta Sanar Da 1 Ga Muharram A Matsayin Ranar Hutu

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana gobe Laraba, 19 ga watan Yuli, 2023 a matsayin ranar ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekara ta Musulunci ta 1445.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye a madadin gwamna Abba Kabir Yusif.

Gwamnan wanda ya taya al’ummar musulmin duniya murnar zagayowar sabuwar shekara ta Musulunci, ya kuma bukaci ma’aikatan gwamnati da sauran al’ummar jihar da su yi addu’ar Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da bunkasa tattalin arzikin jiharmu da kasa baki daya.


Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su rika gudanar da rayuwarsu bisa koyarwar addinin Musulunci tare da yin kyawawan dabi’u na kyautatawa da soyayya da kuma hakuri da juna kamar yadda Annabinmu Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi misali da shi.


Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...