Oluremi Tinubu Ta Ba Da Tallafin Naira Miliyan 110 Ga Iyalin 'Yan Wasan Kano da Suka Rasu
…Gwamna Yusuf Ya Kara Tallafin Naira Miliyan 130, Filaye da Sauran Kayan Jin Kai Uwargidar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ba da tallafin naira miliyan 110 ga iyalan 'yan wasan Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a farkon shekarar nan. Tallafin, wanda aka bayar ta hannun Victim Support Fund, ya bai wa kowanne iyali na mamatan 'yan wasa naira miliyan 5 domin rage musu radadin rashin da suka yi da kuma taimaka musu su farfado da rayuwarsu. A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a na Gidan Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan kyauta daga Uwargidar Shugaban Ƙasa a matsayin “wata alama karara ta nuna jin ƙai, kyakkyawan Shugabanci da tausayi ga ɗan Adam.” A matsayin karin taimako daga gwamnatin jiharsa, Gwamna Yusuf ya sanar da bayar da ƙarin naira miliyan 130. 'Yan wasa goma da suka jikkata sun samu naira miliyan 2 kowannensu da kuma fili,...