Posts

Showing posts with the label Yunwa

Gwamnan Kano Zai Kaddamar da Kashi Na Biyu Na Tallafin Abinci

Image
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin raba buhunan hatsi da kuma baiwa matasa da mata da nakasassu tallafin kudi. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, ya ce, a ci gaba da kokarin gwamnatinsa na bayar da tallafi ga al’ummar jihar domin rage radadin tallafin man fetur, an kammala shirye-shiryen rabon hatsin da suka hada da shinkafa da masara a yankuna 484 dake cikin kananan hukumomi 44 na jihar. Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka a yau a wajen wani taro da shugabannin kananan hukumomin jiha da na kananan hukumomi/Secretries na hudu grassroot Mobilisation platforms (Community Re-Orientation Committee (CRC), Lafiya Jari, Kano PRO-PA da kuma Kwankwasiyya) taron da ya gudana. wanda aka gudanar a dakin taro na Coronation, gidan gwamnatin Kano. Gwamnan ya ce rabon kaso na biyu ya zama wajibi duba da irin matsalolin da mutane ke ciki sannan ya yi kira ga ayyukan rabar a mataki...

'Yan Najeriya Miliyan 25 na cikin barazanar yunwa a Shekara ta 2023

Image
Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, kusan ‘yan Najeriya miliyan 25 zasu fuskanci bala'in yunwa tsakanin watannin Yuni zuwa Agustan wannan shekara ta 2023, muddin ba a dauki matakin gaggawa ba. Adadin dai kari ne kan mutane miliyan 17 da ke cikin hadarin gamuwa da yunwar a Najeriya wanda aka yi hasashe tun a can baya. Sanarwar da Hukumar Bunkasa Ilimin Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a shafinta, ta ce, rikice-rikice da matsalar sauyin yanayi da tashin farashin kayayyakin abinci, su ne ummul-haba’isin jefa ‘yan Najeriyar cikin kangi yunwa. Sanarwar ta ce, an gaza samar da abinci a jihohin Borno da Adamawa da Yobe da ke yankin arewa maso gabashin Najeiya sakamakon tashe-tashen hankula, ga kuma hare-haren ‘yan bindiga a jihohin Katsina da Sokoto da Kaduna da Benue da kuma Niger. Alkaluman da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya NEMA ta fitar sun nuna cewa, matsalar ambaliyar ruwa da aka gani a bara, ta lalata sama da kadada dubu 67...