Posts

Showing posts with the label Shugaban EFCC

Shugaban EFCC Ya Nemi Cin Hancin Dala Miliyan Biyu Daga Wajena - 1 Gwamna Matawalle

Image
Gwamnan jihar zamfara, Bello Matawalle ya zargi shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa da neman cin hancin dala miliyan biyu daga gare shi. Matawalle ya yi wannan zargin ne a wata hira da BBC Hausa a ranar Juma’a, a daidai lokacin da ake ci gaba da takun saka tsakanin gwamnan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa. Idan za a iya tunawa, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Matawalle ya yi kira ga Bawa ya yi murabus, yana mai cewa yana da tambayoyi da zai amsa kan cin hanci da rashawa. Sai dai Shugaban na EFCC ya amsa cewa ba shi da wani abin boyewa yayin da ya bukaci Matawalle da ya kai karar hukumomin da suka dace idan yana da wata shaida a kansa. Duk da haka, da yake magana yayin hirar, Matawalle ya dage cewa ba za a iya amincewa da Bawa ba. Ya ce, “Ba wai kawai a rika zargin gwamnoni ba ne. Ba gwamnoni kadai ke da baitulmali ba, gwamnatin tarayya ma tana da. Me shugaban EFCC yake yi musu? Kamar yadda yake ikirari yana...