Posts

Showing posts with the label Madina

Yanzu-Yanzu: Muhimmiyar Sanarwa Daga Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Kano

Image
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, karkashin Jagorancin Alh, Lamin Rabi'u Danbappa, na sanar da Maniyyatan Da suka fito daga  Kananan hukumomin  1:- Gwarzo   2:- Karaye  3:- Kiru  4:- Shanono  5:- Rogo   6:-Dawakin Tofa  7:-Bagwai  8:-Bichi  9:-Ghari  10:-Tsanyawa   11:- Wudil da Kuma Karamar Hukumar    12:- Gaya. Dasu fito zuwa Sansanin Alhazai na Jiha a Gobe Talata 28-05-2024 da misalin karfe tara na safe 9:00 Domin tantancesu zuwa kasa mai tsarki.       Maniyyatan zasu fito da manya da Kananan jakankunan su tare da tabbatar wa cewa Basu saka komai a cikin Babbar jakar ba.   Allah ya bada ikon fitowa cikin koshin lafiya         Sanarwa daga Sulaiman Abdullahi Dederi Jami'in Yada Labarai da Hulda da jama'a na hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano.

Jami’an NAHCON Dake Makkah Sun Shirya Karbar Alhazan Da Suka Gama Zamansu Na Madinah

Image
Jami’an NAHCON sun shirya tsap don Tarbar Maniyyatan da suka kammala kwanakinsu hudu a Madinah.  A yayin da hakan ya tabbata ne saboda yadda Jami’an suka hada karfi da karfe tsakanin maaikatan NAHCON dake Makkah da wadanda ke Madinah wajen seta duk bukatun da Alhazan ke da Su a Makkah da suka shafi masaukai da wajajen dafa abinci.  A zagayen rangadin da Jami’an suka kai wajen dafa girkin da masaukan Alhazan da anjumar yau dinnan ne za su fara baro Madinah don shigowa Makkah bayan kammala kwanakinsu hudu a Madinah din, kampanonin dake dafa abinci sun tabbatarwa NAHCON za su ciyar da Alhazan ba tare da kwange ba hakazalika masu bada masaukai.  Hakan kuma yasa NAHCON ta sake jaddada lallai idan ba a bai Alhazanta abunda yarjejeniyar da suka rattabawa hannu ba to kampanonin su kwana da sanin za a ma iya soke kwangilar take-yanke.  Zuwa wani lokaci Kadan yau din  ne za a tabbatar da sa idon Jami’an NAHCON zai sa kampanonin bada hid...

Alhazan Kano Sun Kammala Ziyarar Wuraren Tarihi a Madina

Image
Kashi na karshe na Alhazan jihar Kano na shekarar 2023 a kasar Saudiyya sun kammala ziyarar gani da ido a wuraren tarihi a birnin Madina dake a kasa mai tsarki. Shugaban Tawagar 'yan na aikin hajjin Bana, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Madina. Dawakin Tofa ya bayyana cewa rukunin karshe na maniyyata daga Kano sun isa filin jirgin saman Madina lafiya a ranar Alhamis 21 ga watan Yuni, a cikin jirgin Max Air da ke jigilar jigilar mahajjata. Don haka, Alhazan sun samu jagorancin jami’an hukumar Malam Muhammad Ghali Shehu da Malam Aliyu Mukhtar Darma da Gwani Falaki da ke Madina domin gudanar da ayyukansu na addini kamar yadda koyarwar Manzon Allah (SAW) ta tanada. Dawakin Tofa ya yaba da tsarin da Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta yi, wadda ita ce hukumar da ke kula da ayyuka da samar da wuraren kwana da ciyarwa ga daukacin alhazan Najeriya, ciki har da na Kano da ke Madina. Ya kuma baiwa tawagar Ka...

Hukumar NAHCON Ta Ce Ya Zuwa Yanzu Kimanin Maniyyata 33,818 Ne Suka Isa Madina Cikin Jirage 80.

Image
Babban Jami’in dake lura da Ofishin hukumar NAHCON na Madina Sheikh Ibrahim Idris Mahmud ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis a ofishin hukumar NAHCON da ke Madina. Ko’odinetan ya ci gaba da cewa, a cikin wannan lokaci, mahajjata suna gudanar da sallolinsu a masallacin Annabi Muhammad (SAW) tare da ziyartan wasu wuraren ibada da na tarihi. Sheikh Mahmud ya kuma ce hukumar NAHCON ta bude babbar cibiyar Karbar magani a ofishin hukumar da wasu kanana guda uku a wuraren kwana na alhazai domin halartar alhazan da ke bukatar kula da lafiya. Jami’in ya yi nuni da cewa NAHCON tana da kwamitocin sa ido da tantance alhazai da suke zagayawa suna sauraron mahajjata tare da mika rahotonsu ga kwamitocin da abin ya shafa domin gudanar da ayyukan da suka dace, ya kara da cewa tana da burin ganin an kula da bukatun alhazai yadda ya kamata. Ya kuma bayyana cewa a kowane gini akwai manaja a kowane gida da ke daukar alhazai kuma ana sanar da su dakinsa da tu...

Zamu Iya Kwatanta Farin Cikinmu Ne Kadai Da Shiga Aljanna- Inji Mahajjatan Najeriyan Da Suka Je Hajji A Karon Farko

Image
Wata alhajiyar Najeriya, Hauwa’u Sa’ad Joda ta ce shiga aljanna ne kawai zai fi dadi fiye da jin dadin da take ji a halin yanzu yayin da take kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin 2023. A tattaunawar da Jaridar Hajj Reporters ta yi da Joda, wata alhaji daga jihar Adamawa, ita ma ta ce ba za ta iya bayyana yadda take ji ba saboda burinta na rayuwa ya cika. Da take zantawa da manema labarai a ziyarar da ta kai garin Uhud daya daga cikin wuraren da mahajjata suka ziyarta don ganin wasu wuraren tarihi, Hajiya Joda ta bayyana cewa ‘yar uwarta Aisha Ahmad ce ta dauki nauyin gudanar da aikin Hajjin. A cewarta, ta kasa danne kukanta a lokacin da ’yar’uwar ta sanar da ita batun zuwa aikin Hajjin bana, inda ta bayyana cewa “ba za a iya misalta abin farin cikin ba saboda burina na rayuwa ya cika.” Da aka tambaye ta game da ayyukan da Hukumar Alhazai ta Jihar Adamawa da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON suka yi mata daga Najeriya zuwa Saudiyya,  Joda ta ce komai ya tafi cikin...