Posts

Showing posts with the label Oba Bolagun

Gwamnatin Kano ta nada Oba Balogun Da Farfesa Jega, Shugaba Da Uban Jami’ar Sa’adatu Rimi

Image
Majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da nadin Oba Dr. Sanata Moshood Olalekan Ishola Balogun Aliiwo da Farfesa Attahiru Jega, tsohon mataimakin shugaban jami’ar Bayero kuma tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa a matsayin Shugaban da Uban majalisar gudanarwar Jami'ar Ilimi ta Sa'adatu Hakan ya biyo bayan samun amincewa ne daga Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC), wacce ta amince da ita a matsayin jami’ar Jiha ta 61 daga cikin jami'o'in guda 222 a tsarin jami’o’in Najeriya. Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana haka bayan taron majalisar da aka gudanar a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin Kano ya bayyana sauran mambobin majalisar da suka hada da Dr. Muhammad Adamu Kwankwaso, Hajiya Zulaiha UM Ahmed, Dr. Ibrahim Yakubu Wunti, Dr. Halima Muhammad da Alhaji Sabi'u Bako.   Ya ce nadin ya zo daidai da sashe na uku na 22 na dokar Jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi ta Kumbotso wadda ta ce “za a yi