Posts

Showing posts with the label Mutuwa

Yanzu-Yanzu : Matar Alhaji Aminu Dantata, Ta Rasu

Image
Matar hamshakin dan kasuwa na Kano, Alhaji Aminu Alasan Dantata, Hajiya Rabi ta rasu Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa, Hajiya Rabi, mahaifiya ga Tajuddeen Aminu Dantata, ta rasu ne a ranar Asabar. ta bar "yaya biyar  Ta rasu ne sakamakon jinya da ta yi fama da ita  Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Fitaccen dan kwallon duniya, Pele ya mutu

Image
  Fitaccen É—an Æ™wallon nan na duniya É—an Æ™sar Brazil, Pele ya rasu yana da shekara 82. Pele ya rasu ne a ranar Alhamis 29 ga watan Disamban 2022 bayan ya sha fama da rashin lafiya. A kwanakin baya an yi ta yaÉ—a labarin Æ™arya na rasuwarsa. Ya rasu ne sakamakon cutar kansar Æ™aba da kuma cutar Æ™oda Ana ganin Pele shi ne É—an Æ™wallon da ba a taÉ“a samun irin sa ba a duniya, kuma sau uku yana cin gasar kofin duniya wa Æ™asarsa Brazil. Ya ci kofin duniya a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970. A shekarar 2000 ne kuma hukumar Æ™wallon Æ™afar duniya FIFA, ta ayyana shi a matsayin É—an Æ™wallon Æ™arni. Shi ne É—an Æ™wallon da ya kafa tarihin zura Æ™wallaye 1,281 a raga a cikin wasanni 1,363 cikin shekara 21 da ya yi yana buga tamaula. Cikin waÉ—annan har da Æ™wallo 77 da ya ci wa Æ™asarsa cikin wasanni 92 da ya buga wa Brazil É—in. An yi wa Pele tiyata a kan yanke masa kansa a hanjinsa a watan Satumban 2021 a Asibitin Albert Einstein da ke Sao Paulo. An sake kwantar da shi a asibiti a watan Nuwamban 2022. Ƴ...