Alhazan Kano Sun Kammala Ziyarar Wuraren Tarihi a Madina
Kashi na karshe na Alhazan jihar Kano na shekarar 2023 a kasar Saudiyya sun kammala ziyarar gani da ido a wuraren tarihi a birnin Madina dake a kasa mai tsarki. Shugaban Tawagar 'yan na aikin hajjin Bana, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a Madina. Dawakin Tofa ya bayyana cewa rukunin karshe na maniyyata daga Kano sun isa filin jirgin saman Madina lafiya a ranar Alhamis 21 ga watan Yuni, a cikin jirgin Max Air da ke jigilar jigilar mahajjata. Don haka, Alhazan sun samu jagorancin jami’an hukumar Malam Muhammad Ghali Shehu da Malam Aliyu Mukhtar Darma da Gwani Falaki da ke Madina domin gudanar da ayyukansu na addini kamar yadda koyarwar Manzon Allah (SAW) ta tanada. Dawakin Tofa ya yaba da tsarin da Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta yi, wadda ita ce hukumar da ke kula da ayyuka da samar da wuraren kwana da ciyarwa ga daukacin alhazan Najeriya, ciki har da na Kano da ke Madina. Ya kuma baiwa tawagar Ka...