Gwamnatin Kano ta kori 'yan mata biyu daga gidan marayu kan zargin tayar da husuma
Hukumomi a jihar Kano ta kori wasu 'yan mata daga gidan marayu na gwamnatin jihar.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne saboda 'yan matan ba sa bin ƙa'idar zaman gidan tare da ƙoƙarin tayar da husuma tsakanin marayu da ma’aikata.
Sai dai marayun sun ce wasu ma’aikatan gidan ne ke cin zarafinsu ta hanyar ƙoƙarin yin lalata da wasu daga cikinsu.
Ma’aikatar harkokin mata da walwalar al‘ummar ta jihar Kano, ta ce ta kori ‘yan matan biyu daga gidan marayun na Nasarawa ne saboda rashin kiyaye ka’idoji da dokokin zaman gidan.
Sai dai waɗannan ‘yan mata sun ce saboda sun kwarmata lalatar da ake zargin wani ma’aikacin gidan ne ya sa aka kore su, kamar yadda ɗaya daga cikinsu ta shaida wa Majiyarmu
Ta ce ''saboda yana da mabuɗin sito a hannansa, yana ganin kamar shi ke da iko da gidan gaba ɗaya, sai muka je muka gaya wa shugabar gidan, daga baya sai ta zo ta ce ai mun yi masa ƙazafi, daga sai suka rubuta takarda suka kai wa Kwamishina, ita kuma ta bayar da umarnin da a rubuta takarda wai an kore mu, daga baya aka zo aka kira mu aka yi mana wa'azi, cewa mu yadda da ƙaddara mai kyau da marar kyau''
Daga nan sai a ka sanar da su cewa gwamna ya bayar da umarni a kore su daga gidan tun da za su janyo masa matsala kamar yadda ta shaida wa majiyarmu .
Ta ƙara da cewa ''mun ɗauki matakin bayyana abin da ma'aikacin gidan ke yi wa 'yan matan da ke gidan ne, saboda 'yan matan da yake lalata da su 'yan uwanmu ne, dan haka bai makata mu yi shiru ba''
Dan haka a cewarsu bai makata a ajiye ma'aikaci ba amma kuma ya riƙa cin amanar yara da gwamnati.
Daga ƙarshe 'yan matan sun yi kira ga gwamnati da ta shiga cikin lamarin tare da taimaka wa wajen samar musu da wurin zama.
Haka kuma 'yan matan sun ƙaryata batun zargin da ake yi musu na tunzura sauran yara da kuma fita daga gidan kuma ba sa dawowa sai lokacin da suka ga dama, domin kuwa a cewarsu suna zaman lafiya da sauran yaran.
(BBC HAUSA)