Posts

Showing posts with the label EFCC

Ba Zamu Lamunci Yi Mana Katsalandan A Ayyukanmu Ba - EFCC

Image
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta yi kira ga jama’a  cewa laifi ne a hana jami’an hukumar gudanar da ayyukansu na halal. A sanarwar da Shugaban sashen hulda da jama'a na hukumar,  Dele Oyewale  ya sanyawa hannu, yace Sashi na 38(2)(a(b) na dokar kafa hukumar EFCC ya sanya laifin hana jami'an hukumar gudanar da ayyukansu na halal. Masu laifi suna fuskantar daurin kurkuku na kasa da shekaru biyar. Wannan gargadin ya zama dole bisa ga yadda mutane da kungiyoyin da Hukumar ke bincike ke kara ta'azzara na daukar doka a hannunsu ta hanyar daukar 'yan baranda domin dakile ayyukan EFCC. A lokuta da dama, jami’an Hukumar sun yi taka-tsan-tsan wajen tunkarar irin wannan tada zaune tsaye domin gujewa tabarbarewar doka da oda. Abin takaici, ana É—aukar irin wannan halin a matsayin alamar rauni. Don haka hukumar ta yi gargadin cewa daga yanzu ba za ta lamunci duk wani yunkurin wani mutum ko kungiya na kawo cikas ga ayyukanta ba domin ...

EFCC Ta Kwace Fasfon Sadiya Da Betta Edu

Image
Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta kwace fasfo din tsohuwar Ministar aJin-kai, Betta Edu da magabaciyarta, Sadiya Umar-Farouq, kan binciken badakalar da ake yi a ma’aikatar. Wata majiya mai tushe daga EFCC ta ce an kwace fasfo din Edu da da Sadi ya  ne domin hana su fita daga Najeriya yayin da ake ci gaba da binciken. “Hukumar ta kwace fasfo din tsofaffin ministocin biyu, Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu. “Mun kuma kwace fasfo din Halima Shehu har sai an kammala bincike. Hukumar ba ta son yin kasadar ganin ko daya daga cikinsu ya fice daga Najeriya alhalin ana bincike a kan su,” in ji majiyar. Dangane da binciken Edu da Sadiya Umar-Farouq, EFCC ta gayyaci shugabannin bankunan Zenith, Providus da Jaiz ofishinta a ranar Talata. Ita ma Halima Shehu, wacce aka dakatar daga hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa, EFCC na bincike a kan ta. Aminiya  ta ruwaito cewa Edu ta isa hedikwatar EFCC da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata domin amsa...

Sojoji Sun Kutsa Ofishin EFCC Dake Kuduna Domin Kubutar Da Abokan Aikinsu

Image
Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami'an sojin saman ƙasar suka kutsa ofishinta da ke Kaduna domin ƙwato 'yan uwansu da hukumar ta tare bisa zargin 'karya dokar aikin tsaro'. Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun jami'ain hulɗa da jama'a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba jami'an EFCC sun kama wasu mutum biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuɗi ta intanet a unguwar Barnawa da ke birnin Kaduna Hukumar ta ce ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida - da suka haɗar da sojoji huɗu da ɗaliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu - waɗanda ke wurin a lokaci da aka kama waɗanda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna ƙawanya da nufin tilasta sakin mutanen. ''Daga nan ne kuma aka kama su tare da tsare su a ofishin hukumar,...

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Dakatar Da Hukumomin EFCC, ICPC Da CCB Daga Bincikar Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Kano

Image
A ranar Litinin din da ta gabata ce wata babbar kotun jihar Kano ta hana Hukumar EFCC  da Hukumar da'ar ma'aikata da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka (ICPC) shiga harkokin Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano. Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa EFCC da CCB sun rubuta wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar wasika inda suka bukaci a binciki ayyukanta da na shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimingado. A cewar umarnin kotun, wadanda suka shigar da kara sun hada da babban lauyan gwamnatin jihar Kano, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, da Barista Muhuyi Magaji Rimingado. Yayin da wadanda ake kara sun hada da EFCC, CCB da ICPC A wani umarnin kotu da ya bayar a ranar Litinin mai shari’a Farouk Lawan Adamu ya ce an bayar da wannan umarnin ne ta hanyar umarnin wucin gadi na hana wadanda ake kara ko dai su kansu, ko wakilai, ko ma’aikata, ko kuma duk wanda ya gayyato, barazana, kora, kora, kam...

Yanzu-Yanzu : Shugaban Bola Ahmed Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban Hukumar EFCC

Image
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya amince da dakatar da Mista AbdulRasheed Bawa, CON a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC domin ba da damar gudanar da bincike mai inganci a kan yadda ya gudanar da aikinsa yayin da yake rike da mukamin  Hakan ya biyo bayan zarge-zargen cin zarafi da ake yi masa. An umurci Mista Bawa da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Daraktan Ayyuka a Hukumar, wanda zai kula da harkokin ofishin Shugaban Hukumar har sai an kammala bincike. NTA

EFCC Ta Kammala Shirin Kama Wasu Gwamnonin Najeriya

Image
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, wato EFCC ta kaddamar da gagarumin bincike akan wasu Wani bincike da Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya ta gudanar, yace Hukumar EFCC ta baza komarta domin cafke wasu daga cikin gwamnonin da mataimakansu 28 dake shirin sallama da gidajen gwamnati a makon gobe.  Binciken yace tuni EFCC ta bukaci takardun kadarorin da wadannan gwamnoni suka cika kafin fara aiki, wanda ya bayyana irin dukiyar da suka mallaka a wancan lokaci, yayin da kuma take dakon wadanda zasu bayar ayanzu domin nazari akansu.  Jaridar tace hukumar tayi shiri tsaf domin ganin wadannan gwamnoni basu gudu sun bar kasar ba, bayan mika mulki ga wadanda zasu gaje su a ranar litinin mai zuwa.  Ko a makon jiya, shugaban hukumar Abdurasheed Bawa, ya dada jaddada shirin EFCC na bin diddigin wadannan gwamnoni da mataimakansu dake shirin sauka, sakamakon korafe korafe da kuma zarge zargen da ake musu da rub da ciki da kudaden talakawa. ...

Shugaban EFCC Ya Nemi Cin Hancin Dala Miliyan Biyu Daga Wajena - 1 Gwamna Matawalle

Image
Gwamnan jihar zamfara, Bello Matawalle ya zargi shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa da neman cin hancin dala miliyan biyu daga gare shi. Matawalle ya yi wannan zargin ne a wata hira da BBC Hausa a ranar Juma’a, a daidai lokacin da ake ci gaba da takun saka tsakanin gwamnan da hukumar yaki da cin hanci da rashawa. Idan za a iya tunawa, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Matawalle ya yi kira ga Bawa ya yi murabus, yana mai cewa yana da tambayoyi da zai amsa kan cin hanci da rashawa. Sai dai Shugaban na EFCC ya amsa cewa ba shi da wani abin boyewa yayin da ya bukaci Matawalle da ya kai karar hukumomin da suka dace idan yana da wata shaida a kansa. Duk da haka, da yake magana yayin hirar, Matawalle ya dage cewa ba za a iya amincewa da Bawa ba. Ya ce, “Ba wai kawai a rika zargin gwamnoni ba ne. Ba gwamnoni kadai ke da baitulmali ba, gwamnatin tarayya ma tana da. Me shugaban EFCC yake yi musu? Kamar yadda yake ikirari yana...

Duk wanda ya kwarmata masu É“oye sabbin kuÉ—aÉ—e zai samu tukuici – EFCC

Image
Hukumar yaÆ™i da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce bankunan kasuwanci ne suka janyo tarnaÆ™i wajen ganin sabbin kuÉ—i sun wadata a hannun jama'a. EFCC ta ce bayanai daga Babban Bankin Najeriya sun nuna cewa zuwa yanzu, CBN ya buga sabbin takardun kuÉ—i sama da naira biliyan 400, amma bankuna sun Æ™i fitarwa su bai wa jama'ar Æ™asar. Shugaban hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa a wata tattaunawa da BBC, ya buÆ™aci 'yan Najeriya su tona asirin masu É“oye sabbin kuÉ—i, don ganin hukumar ta je ta Æ™wace su. Abdurrashe Bawa ya ce wannan ita ce mataki na gaba da suke ganin zai taimaka wajen kawo wa talakan Najeriya waraka. Sannan ya tunasar da cewa akwai tukuici mai gwabi ga duk mutumin da ya taimaka aka gano wurare ko mutumin da ke rike da sabbin kudade. 'Ma’aikatan banki ne matsalar mu’ Shugaban na EFCC ya ce babu shaka sun yi na'am da wannan sauyi kuÉ—i, saboda bayanan sirri ya nuna musu cewa akwai mutane da dama da suka boye kuÉ—aÉ—e, suna cinikayya a boye. Sai...

Mutum 26 Sun Saye Kadarorin Diezani Da Aka Yi Gwanjonsu

Image
Akalla mutum 26 ne suka saye kadarorin da gwamnati ta yi gwanjonsu bayan kwato su daga hannun barayin gwamnati. Kadarorin sun hada da gidaje da filaye da aka kwato daga tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Allison-Madueke, a Abuja da sauran wurare. A shekarar da ta gabata Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta yi gwanjon kadarorin ga masu son sayen su. Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, a ranar Litinin hukumar ta fara mika kadarorin da aka saye na Legas da Abuja da Fatakwal da Kano da sauran wurare. Sai dai kadarorin sun yi kwantai a ranar Liinin da aka yi gwanjon su, ko mutum guda ba a samu da ya sayi ko da daya daga cikinsu ba. Amma mutum shida daga cikin 90 da suka nema suka yi nasara a rukuni na hudu a ranar Talata. Da yake sanar da wadanda suka yi nasara a ranar Alhamis, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce kadarori 26 sun samu shiga, 13 kuma sun gaza, saboda rashin cika ka’ida da sauransu. A cewar Uwujaren, “Kadarori 39 ne a rukuni na biyar wadanda ke a wurare da...

EFCC Ta Yi Gwanjon Kadarorin Su Diezani A Kasuwa

Image
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sanar da yin gwanjon wasu kadarorin da ta kwace daga hannun ’yan siyasa da ’yan kasuwa ga ’yan Najeriya masu bukatar saya. Hukumar ta ce kadarorin dai na jibge ne a Jihohin Legas da Ribas da Abuja da Anambra da Gombe da Ebonyi da Kaduna da Delta da Edo daKwara da Kuros Riba da Osun da kuma Oyo. Aminiya ta gano cewa daga cikin kadarorin har da na tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Allison-Madueke, wadanda hukumar ta ce an mallake su ta haramtacciyar hanya. A wata sanarwar da hukumar ta wallafa ranar Asabar, EFCC ta ce daidaikun mutane da kuma kamfanoni da kungiyoyin da ke son sayen kayan da aka yi gwanjon dole ne su kasance ba a taba daure su ba a baya. A cewar sanarwar, ga masu bukatar sayen kadarorin, za su iya cike fom din neman saye da za a iya samu a shafin hukumar na www.efcc.gov.ng, kafin daga bisani a gayyace su don ganin kadarorin da ido. Kadarorin da aka yi gwanjon nasu sun hada da wani gida a rukunin gidaje na Herit...