Posts

Showing posts with the label Mele Kyari

Yanayin Kasuwa Ne Ya Sa Man Fetur Ya Kara Tashi — NNPC

Image
Shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya danganta tashin farashin man fetur daga Naira 540 zuwa Naira 617 da yanayin kasuwa. Ya bayyana haka ne ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Talata, bayan wata ganawa da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima. “Farashin ya danganta da yanayin kasuwa. Wannan shi ne ma’anar tabbatar da cewa kasuwa ta daidaita kanta. Farashin zai iya hawa kuma a wani lokacin zai iya sauka. Ba batun samar da mai ba ne. “Idan ka je kasuwa, ka sayi kaya, za ka zo kasuwa ka sayar da shi a kan farashin da kasuwa ta ke. Ba shi da alaka da wadatarsa. Mun samu sama da kwanaki 32 muna shigo da mai. Wannan ba matsala ba ce,” in ji shi. Kyari, ya ce abu ne mai kyau ga ‘yan kasuwa su daidaita farashin. “Ina tabbatar wa ’yan Najeriya cewa wannan ita ce hanyar da ta dace don daidaita farashin yanayin kasuwa. Ba ni da cikakken bayanai a wannan lokacin, amma na san cewa wannan ba mai dorewa ba ne. Na san cewa kamfanoni da yaw

A Watan Maris Za A Fara Hako Man Fetur A Jihar Nasarawa – NNPC

Image
Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya ce a watan Maris Mai zuwa zai fara aikin hako danyen man fetur a karo na farko a Jihar Nasarawa. Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana hakan ranar Juma’a, lokacin da ya karbi Gwamnan Jihar, Injiniya Abdullahi Sule da kuma wata tawaga daga Jihar a ofishinsa. Gano man a rijiyar Keana ta Yamma da ke Jihar ta Nasarawa na zuwa ne kasa da wata biyar bayan kamfanin ya fara hakar wani a rijiyar Kolmani da ke tsakanin Jihohin Bauchi da Gombe. A cikin sabuwar sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, NNPC ya ce, “A ci gaba da aikinsa na gano man fetur a yankunan tsandauri na Najeriya, kamfanin zai fara aikin hako mai a rijiya ta farko a Jihar Nasarawa a watan Maris na 2023.” Jaridar Aminiya ta ruwaito} Mele Kyari ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya tabbatar da akwai man fetur din dankare a yankin. Daga nan sai ya bukaci a gaggauta fara aikin saboda ya ce sannu a hankali duniya ta fara dawowa daga rakiyar man fetur zuwa makamashin da ba ya lal